Banza ta fadi: Tsananin yunwa ta sanya mutane daka wawa akan motar giya a lokacin da ta fadi

0
356

Anyi asarar miliyoyin nairori a lokacin da babbar tirela dauke da katan-katan na giya (barasa) ta fadi a Ekwukobia, a jihar Anambra.

Lamarin da ya faru a ranar Juma’a, 8 ga watan Mayu, mutanen da suke zaune a wannan yanki, sun ga hakan a matsayin wata dama da zasu sha giya su more.

A bidiyon da yake ta yawo a shafukan sadarwa, an nuno mutanen yankin suna daka wawa akan kwalaben giyar, inda suke murnar banza ta fadi.

https://www.instagram.com/p/B_9t985H0eP/?utm_source=ig_web_copy_link

Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake fama da dokar hana fita daga gida da gwamnati ta sanya a jihar ta Anambra, domin dakile yaduwar cutar Coronavirus a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here