Bankin duniya ya bawa Najeriya rancen dala miliyan 750 don gyaran wutar lantarki

0
362

Bankin Duniya ya amince ya bawa gwamnatin tarayyar Najeriya rancen dala miliyan 750 ($750m), don amfani da shi wajen gyara wutar lantarki a Najeriya.

A wata sanarwa da bankin duniyar ya fitar a yau Laraba, 24 ga watan Yuni, ya ce bashin za ayi amfani dashi ne wajen gyara wutar lantarki a Najeriya.

A cewar bankin gyaran da za a yiwa wutar lantarkin zai tabbatar da an samu 4,500MWh na wutar lantarki ga kamfanonin da suke raba wutar lantarkin daga nan zuwa shekarar 2022.

Diraktan bankin duniyar na Najeriya, Shubham Chaudhuri, ya ce samun ingantacciyar wutar lantarki a Najeriya zai cire mutane miliyan 100 daga talauci.

“Rashin ingantacciyar wutar lantarki shine ya kawo cikas ga ayyukan tattalin arziki da kuma masu saka hannun jari da samar da ayyukan yi, inda gyara wutar zai taimaka wajen cire ‘yan Najeriya miliyan 100 daga talauci.

“Manufar wannan aiki shine taimakawa wajen gyara wutar lantarki don tabbatar da ita akan hanyar da ta dace. Wannan yana da matukar muhimmanci a daidai wanna lokacin da gwamnati take bukatar duk wata hanya da za ta samu wajen kare rayukan al’umma wajen samar da abubuwan more rayuwa,” cewar sanarwar.

A cewar bankin duniyar, kusan kashi 47 cikin dari na ‘yan Najeriya ba su da wutar lantarki, haka kuma wadanda suke samun wutar ma suna fama da yankewar wuta a lokuta da dama.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here