Banda abinci babu wani magani da suke ba mu – Cewar saurayin mai cutar Coronavirus

0
364

Wani saurayi da aka sallama daga wajen kula da masu cutar coronavirus a jihar Neja, ya bayyana yadda rayuwarsu ta kasance a wajen.

A wata hira da yayi da jaridar The Nation, marar lafiyan wanda aka sallama daga asibiti a jiya 24 ga watan Mayu, ya ce har suka kammala zamansu a wannan waje babu wata kwaya da aka basu da sunan magani.

Ya ce duk da cewa an tabbatar da suna da cutar, amma babu wani magani da aka yi musu, kuma lokacin da za a sallame su ba a sake yi musu gwaji ba kawai ance su tafi ne.

Daya daga cikin marasa lafiyan da aka dauko daga garin Zumba, cikin karamar hukumar Shiroro, ya ce yana tunanin za a bashi magani a kuma kula da lafiyarsa a wannan waje, amma shi abinda ya san ake bashi abinci ne kawai.

“Na yi tunanin za a duba lafiya ta a bani magani sosai, amma banda abinci babu wani abu da suke bamu da sunan magani. Hatta paracetamol wannan basu bamu ba har muka gama kwanaki 14,” cewar saurayin da ya nemi a boye sunanshi.

Haka kuma ya bayyana mahaifiyarsa da ‘yan uwansa da suma aka dauke su saboda kamuwa da cutar, suma ba ayi musu wani magani ba. Ya ce bayan an sallame su ko kudin mota ba a basu ba kawai ance su tafi gida an sallame su.

“Kawai sun zo sun ce mana mu tafi gida an sallame mu. Ba su damu da yadda zamu koma gida ba ko akwai kudi a hannunmu ko babu. Mun yi tafiya mai nisa a kasa kafin mu samu wani ya dauke mu a mota bashi sai da muka je Zumba muka ari kudi muka biya.”

Ya zuwa yanzu dai jihar Neja na da mutane 26 da suka kamu da cutar, inda mutane 18 ke kwance a asibiti, biyar sun warke daya kuma ya riga mu gidan gaskiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here