Ban yafe ba: Dino Melaye yayi tsinuwa akan duk wanda ya boye shinkafar da ya bayar a rabawa talakawa

0
345
  • Tsohon sanata mai wakiltar jihar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayar da buhunhunan shinkafa taimako ga marasa karfi
  • Dino Melaye ya ce wannan shinkafa ya bayar da ita ne domin marasa karfi su amfana, inda yace baya so masu rabawa su boye shinkafar a gidajensu
  • Tsohon Sanatan ya ce wannan shinkafa za a raba ta ba tare da la’akari da jam’iyya ba, kuma kowa zai samu

Fitaccen dan siyasar Najeriya, Dino Melaye, ya bayar da tallafi ga marasa karfi a yankinsa a wannan lokaci da mutane ke cikin wani hali.

A wani gajeren bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis 7 ga watan Mayu, tsohon Sanatan ya ce zai bayar da buhunhunan shinkafa ga marasa karfi na yankin jihar Kogi ta Yamma.

Haka kuma yayi gargadi ga masu raba shinkafar, inda ya ce baya so kowa ya boye wannan shinkafa a gidan domin kuwa ta talakawa ce, ya kara da cewa Allah zai kama duk wanda yaci amanarshi.

Dino ya ce za a raba shinkafar ne ba tare da la’akari da jam’iyya ba, a cewarshi duk mutanen da suke yankin da za ayi rabon shinkafar za su samu wannan shinkafa.

Haka kuma a kwanakin baya wani bidiyo yayi ta yawo da ya nuna Dino Melaye yana rabawa masu tallar ayaba kyautar kudi, inda ya basu shawara akan su bi doka su zauna a gida a wannan lokaci na Coronavirus.

Kafin ya basu kudin sai da yayi musu nasiha mai tsawon gaske akan yadda suke sanya kansu cikin hadari kan fitar da suke yi a wannan lokaci.

Ya ce baza su san lokacin da za su dauki cutar ba. Wata mace da take sayar da ayabar ta bayyana cewa duk da ta san hadarin da rayuwarta ke ciki, amma rashin kudi yasa baza ta iya zama a gida ba.

Ta ce tana da yara guda shida, kuma ba za iya zama ta cigaba da ganinsu suna kukan yunwa ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here