Ban mallaki gida ko guda 1 ba a duniyar nan tun da na hau Minista – Isa Ali Pantami ya yi martani

0
455

Ministan sadarwa na Najeriya, Dr Isa Ali Pantami, ya karyata wasu rahotanni da ake ta yadawa a wasu kafafen sadarwa na yanar gizo dake nuni da cewa ministan ya sayi wasu sababbin gidaje da ya sanya iyalan shi a ciki.

A jiya Juma’a ne 3 ga watan Yuli, ministan ya bayyana haka ta bakin mai magana da yawunsa, Uwa Suleiman.

Ta ce ya kamata kowa ya sani, yawan kudin da Pantami yake samu a wannan lokacin da yake kan kujerar minista bai kai yawan kudin da ake biyansa a lokacin da yake aikin koyarwa a jami’ar Madina ba.

Haka kuma ta kara da cewa, ba wai duniya ce a gabansa, ya karbi mukamin ne kawai domin ya taimakawa Najeriya.

Uwa ta bayyana cewa: “Dr Isa Ali Pantami, yana daya daga cikin ‘yan Najeriya da basu damu da duniya ba, tsananin kishin kasa da son taimako ne ya sanya ya dawo Najeriya ya karbi mukamin nan lokacin da aka neme shi.

“Domin bayyana gaskiya, ministan bai sayi gida ko guda daya ba a duniya tun bayan hawan shi kujerar minista.”

Ta cigaba da cewa: “Gidajen da aka wallafa aka ce ministan ya siya daya daga cikinsu wanda yake zaune a ciki ne tun watan Janairun shekarar 2017, sama da shekara 2 kafin ya hau kujerar minista.

“Dayan kuma haya yake yi, wanda ya karba tun a ranar 17 ga watan Disambar, 2019.

Jaridar Sahara Reporter ce dai ta sanya hotunan wasu katafarun gidaje, inda ta bayyana cewa ministan ya sayi gidajen ya sanya matayensa guda uku a ciki a Abuja.

Ga dai hotunan gidajen:

Daya daga cikin gidajen da aka ce Pantami ya saya a Abuja | Hoto: Sahara Reporters
Daya daga cikin gidajen da aka ce Pantami ya saya a Abuja | Hoto: Sahara Reporters

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here