Idan ana magana game da yara mata kanana, a wasu kasashen Musulman na duniya ba a duba shekaru a wasu abubuwan. Shekaru suna da matukar muhimmanci, saboda bawai yana sanya yara suyi hankali bane kawai, yana taimakawa wajen samun daidaito a jikinsu da kaiwa minzalin balaga.

Wani lamari da ya faru mai ban tausayi da ya faru sakamakon watsi da aka yi da yanayi na shekaru ya jawo kace-nace. Labari ne na wata yarinyar ‘yar shekara 8 daga kasar Kuwait wacce aka aurar a kasar Yemen, ta mutu a darensu na farko da angonta, bayan yayi mata ila a lokacin saduwa da ita.

Yanzu dai kafin mu cigaba, mutane suyi tunani a matsayinsu na masu tunani, ba tare da hange a bangaren addini ko al’ada ba. Yarinya ‘yar shekara 8 wacce ko balaga bata yi ba, ita ce aka aurar ana so ta biyawa mijinta bukata a bangaren jima’i, shin wannan abu ne mai kyau kuwa?

Amaryar mai suna Rawan, an ruwaito cewa ta mutu bayan jini yayi ta fita daga gabanta, sakamakon gabanta da y samu matsala sanadiyyar saduwa da ita da mijinta yayi a daren su na farko.

Masu rajin kare hakkin dan adam a kasashen Yemen da Kuwait sun bukaci hukumomi da su dauki mummunan mataki akan wannan ango, wanda ya auri yarinyar, kuma ya sadu da ita duk da ya san cewa ba ta kai minzalin hakan ba.

Haka kuma sun bukaci hukumomi da su dauki mummunan mataki akan dangin yarinyar, wadanda suka aurar da ita a mataki na wannan shekarun, duk da sun san cewa bata kai mataki na saduwa da namiji ba.

An ruwaito cewa angon yarinyar ya ninka shekarunta kusan sau sau biyar ko sau shida. Hakan na nufin yana da kimanin shekaru 40 har da doriya.

Lamarin ya jawo kace-nace sosai a shafukan sadarwa, inda aka dinga zagin angon, sannan aka dinga yiwa yarinyar addu’a da kuma rokon bi mata hakki akan wannan zalunci da aka yi mata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

7 COMMENTS

 1. Ba a san dalilin da yasa akayi wannan aure ba.
  Amma tabbas wannan ango ya aikata dabbanci wadda bai kamata ace hukumomin kasa da kasa sun kyale shi. Ya kamata a dauki mummunan mataki akansa har da su iyayen yarinyar.

 2. Subhan Allah
  Gaskiya wannan baidaceba,duba da yanayin damuke ciki wanda ba amfani da kissan magabata yakamata abi ba saidai yanayin cika da kamala da kuma yanayin girman jiki wato kosawarta.
  Allah yasauwake.

 3. Kai Amma Allah ya ji kanta, Kuma tayi nasara wallahi ta mutu a dakin ta na auren sunnah Wanda ba addinin sune ya hana ba.

  • Hauka ya cika maka Kai,yarinya Yar shekara 8 me ta sani da kake maganar ta mutu a dakin mijin ta ?Kamata yayi a kama iyayen ta a killer don sunyi kisan Kai gobe wani shege ya kuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here