Bakin talauci ne ya saka na sayar da jaririna N130,000 – Cewar budurwa ‘yar shekara 20 da ta zabi kudi akan dan da ta haifa

0
165
  • Asirin wata budurwa mai shekaru 20 kacal a duniya ya tonu, bayan an kamata ta sayar da jaririn da ta haifa
  • Budurwar dai ta sayarwa da wasu mace da namiji jaririn da ta haifa dinne mai kwanaki 28 kacal a duniya akan kudi naira 130,000
  • Bayan an cafke su jami’an tsaro sun bayyana cewa wannan ba shine karo na farko da budurwar ta saba haifar jariri ta sayar ba

Wata budurwa mai suna Miracle Kalu, wacce ke da shekaru 20 kacal a duniya, taje anyi mata ciki a titi, sai dai bayan ta haifi dan ta dauke shi ta kai kasuwa ta sayar akan kudi naira 130,000.

Sai dai dama ance Allah ba azzalumin bawansa bane, domin kuwa ta shiga hannun jami’an tsaro ita da abokanan harkallarta.

Kalu wacce ta fito daga garin, Ohafia, cikin jihar Abia, ta ce rashin kudin da za ta lura da kanta ne da dan nata ya saka ta sayar da jaririn nata mai kwanaki 28 kacal a duniya.

Budurwar ta ce bayan ta dauki cikin, saurayinta, wanda bata san inda gidansa yake ba yaki amincewa da cikin nashi ne.

Asirin ta ya tonu ne dai bayan an kama abokanan harkallarta guda biyu, Patrick Mbama, mai shekaru 41 da Ogechi Ekwebele mai shekaru 30, a jihar Legas a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga jihar Imo.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ce jaririn na ta kuka a cikin motar, inda hankalin kowa ya dawo kan jaririn da wacce ake tunanin mahaifiyarshi ce, suna rokonta akan ta shayar da shi, hakan ya saka suka fara zarginta, bayan taki ta shayar da shi.

Odumosu ya ce: “Bayan gabatar da bincike a kansu, wadannan mutanen sun bayyana cewa sun biya kudin jaririn.” Kalu wacce tayi magana da manema labarai, ta ce ita marainiya ce ko makarantar sakandare ba ta gama ba.

Sai dai kuma jami’an ‘yan sandan sun ce dama can halayyarta ce ba yanzu ta fara haihuwa ta sayar da jariri ba.

Mutane na farko Mbama da Ekwebele sun sanyi jaririn akan kudi naira 130,000 daga hannun Kalu, inda kuma suka sayar da shi naira 150,000 ga wasu mutane masu suna Izuchukwu Okafor mai shekaru 51 da Cecilia Okafor mai shekara 40 a jihar Legas.

Okafor ta ce tsananin son samun da ne ya sanya ta sayi wannan jariri. “Shekaru 15 ba tare da haihuwa ba, ba karamin abu bane,” ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here