Fitacciyar jarumar Kannywood Hannatu Bashir wacce aka fi sani da Hanan ta aika da wata tambaya ga abokanan sana’arta a shafin ta na Instagram, inda ta bukaci a mata karin bayani.

Jarumar ta wallafa cewa ga wata tambaya nima tambayata aka yi, shin da gaske ne ba dan mai kudi a Kannywood? Ta kara a kasa da cewa tambaya ce fa.

Wasu daga cikin jaruman sun bata amsa, inda mafi yawancin su ke cewa hakane dukkansu ‘ya’yan talakawa ne a cikin masana’antar suka samu kudaden su.

Idan ana magana ta kudi da talauci ana magana ne akan matakai kala-kala, akwai hamshakan masu kudi, akwai masu kudi, akwai kuma masu rufin asiri, kafin azo ga talakawa.

Saboda haka zamu iya cewa ‘ya’yan hamshakan masu kudi ne babu a masana’antar, amma akwai da yawa wadanda suka fito daga gidaje na rufin asiri.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here