Fitaccen mai arzikin nan na kudancin Najeriya, Arthur Eze ya ce Allah ne kadai zai iya bawa dan kabilar Igbo shugabancin Najeriya.

A wata hira da yayi da manema labarai a Anambra ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, Eze ya ce Igbo basu da hadin kai kuma basa kaunar junansu ko kadan.

A cewar shi, ‘yan arewa ne suka sanya shi a kasuwancin man fetur, suka bude mishi hanya sosai yayi arziki ba tare da sun san shi ko la’akari daga inda ya fito ba. Ya ce bai tunanin dan kabilar Igbo zai taba yin haka ga wata kabilar.

A zancen shi Eze ya ce:

“Dole sai Igbo sun fara nunawa junansu soyayya kafin su shugabanci kasar nan. Shin suna ma kaunar junansun? ‘Yan Arewa suna da karamci. Idan kaje Arewa, za ka ga coci a ko’ina. Akwai coci a Kano, Sokoto, Kaduna, Abuja da sauransu, amma duk da haka sunce ‘yan Arewa sun tsane su. Shin mu Igbo muna kaunar junanmu?

“Allah ne kawai zai iya bawa dan kabilar Igbo shugabancin Najeriya. Mu yi addu’a Allah yasa mu samu Igbo wanda yake da zuciyar taimakon al’umma. Na fi son mutumin da yake da tausayi, da zai dinga tunawa dani, babu ruwana daga inda ka fito.

“Naje arewa, basu san ko wanene ni ba. Sun bani dala miliyan 12 don gina gidan talabijin Kano a shekarar 1980. Bani da ko sisi a wancan lokacin. Haka kuma ya faru a Katsina, Borno da Kaduna. Daga nan suka sanya ni a harkar kasuwancin man fetur. Basu damu daga inda na fito ba. Ku gaya mini idan akwai wani Igbo da zai iya yin irin wannan?”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here