Babu wani uzuri da zan kara dauka daga wajenku – Buhari ga Hafsoshin tsaro

1
1320

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa matuka akan matsalar tsaro a Najeriya, musamman a yanzkin arewacin kasar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Wannan dai ya fito daga bakin mai bawa shugabanb kasar shawara a fannin tsaro, Manjo-Janar Babagana Munguno, bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa

Munguno ya sanar da ‘yan jarida na gidan gwamnatin shugaban kasar cewa shugaba Buhari ya nemi shugabannin tsaron da su kara dagewa tukuru wajen kawo karshen matsalar tsaron.

Ya kara da cewa shugaban kasar yace, ya san shugabannin tsaron suna bakin kokarinsu, sai dai yana ganin akwai alamun sunyi kasa a gwiwa wurin kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Najeriya.

Shugaban kasar ya ce daga yanzu ba zai kara daukar wani uzuri daga wajen hafsoshin tsaron ba, dan haka kowanne daga cikinsu yayi duk wani abu da ya kamata wajen kawo karshen matsalar.

Haka kuma shugaban kasar ya nuna rashin jin dadinsa akan matsala ta rashin hadin kai dake faruwa tsakanin hukumomin tsaron a Najeriya, ya bukaci su hada kai don kawo karshen matsalar.

Shugaban kasar kuma yayi kira ga ofishin NSA akan ya gana da gwamnonin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da kuma gwamnan jihar Neja akan yadda za a kawo karshen matsalar a yankinsu da ‘yan bindiga suka addaba.

Press Lives ta kawo muku rahoton cewa shugaban kasar ya shiga ganawar sirri da hafsoshin tsaron a safiyar yau Alhamis dinnan 18 ga watan Yuni, 2020 a cikin fadarsa dake babban birnin tarayya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

  1. Magana ta gaskiya itace kawai aciresu a jarraba da wasu. Wlh Nigeria tana cikin hadari sosaifa . Yakamata adubi lamarin tunmuna game JUNANMU

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here