Babu wanda ya isa ya hana Almajiranci a Najeriya – Sheikh Dahiru Bauchi

0
418

Fitaccen Malamin Darikar nan na Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauhci, ya ce shirin da gwamnonin Arewa suke yi na hana Almajiranci ba za a taba amincewa da shi ba.

Malamin ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da The Sun, yana mai jadadda cewa wadanda ke yin amfani da tsarin suna da ‘yancin yin hakan a karkashin kundin tsarin mulkin kasa, wanda ya bawa kowanne dan kasa ‘yancin gudanar da addini.

“Tsarin mulkin kasar nan ya ba mu ‘yancin gudanar da addininmu yadda muke so. Kur’ani shine jigon komai a addininmu. Tunda Kur’ani ya basu (wadanda suke da iko) dokoki suka ki su bi, wane hakki ne da su da za su bayar da umarni ko doka ga Kur’ani? Saboda haka ba za mu amince da haramta Almajiranci da gwamnoni suka yi ba,” in ji shi.

“An tauye mana ‘yancin mu na yin bauta. Ba za mu taba yadda da tauye mana hakki na zuwa ko ina a fadin kasar nan don gudanar da addini ba.

“Dalilin shine akwai gwamnati, kuma gwamnati tana aiki da tsarin mulki. Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bawa kowanne dan kasa ‘yancin zuwa duk inda yake so, sannan ya bawa kowa damar gudanar da addini. Wadannan Almajiran ‘yan Najeriya ne.

“Tattaro mutanen mu kamar dabbobi daga wani wuri zuwa wani wuri, ba za mu taba yarda da hakan ba. A matsayinmu na ‘yan Najeriya, muna da ‘yancin aiwatar da addininmu. Kur’ani shine tushen addininmu. Ba za mu yarda da wani tauye hakki ba.

“Ba za mu yarda da haramta almajiranci ba. Muna da hakkin zuwa ko’ina a cikin duniya don karanta Kur’ani.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here