Babu ruwana duk wanda na kama ya kai dan shi almajiranci sai yayi gidan yari – El-Rufai

0
306

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewa duk iyayen da ya kama sun aika dan su almajiranci shi ma zai tura su gidan yari ne tsawon shekara biyu.

El-Rufai ya bayyana hakane a jiya Litinin a lokacin da ya ziyarci almajirai 200 da aka dawo dasu daga jihar Nasarawa ake gabatar da gwajin cutar coronavirus a kansu a makarantar sakandare ta Kurmin Mashi dake jihar ta Kaduna, kamar dai yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

Haka kuma gwamnan ya ce duk malamin da ya kama yana koyar da yara almajiranci sai an hukuntashi an kai shi gidan yari, sannan kuma zai biya N100,000 ko N200,000 akan kowanne almajiri guda daya.

Ya ce duka almajiran da aka kawo daga wasu jihohi na Najeriya duka ‘yan asalin jihar Kaduna ne, saboda haka gwamnati za ta basu hanyar da za su samar da cigaba ga kansu da jihar.

A cewar shi jihar Kaduna za ta yi iya bakin kokarinta wajen ganin ta basu kulawa sun zama wasu a nan gaba.

“Saboda haka zamu cigaba da karbar duk almajiran jihar Kaduna domin gyara musu hali, sannan mu sanya su a makaranta mafi kusa da inda iyayensu suke zaune.

“Zamu cigaba da yin haka har sai mun kawo karshen almajiranci a jihar Kaduna, wanda ba ilimi bane hanya ce kawai ta cin zarafin yara da kuma bata musu rayuwa.

“Babban burinmu shine mu basu ilimin boko ba tare da hana su damar samun ilimin addini ba.

“Za su cigaba da karatun Al-Qur’ani amma a karkashin kulawar iyayensu ba wai a karkashin wanda bai san su ba.”

Ya yi bayanin cewa Ma’aikatar Ayyukan Jama’a da cigaban Jama’a (MHSSD), tare da hadin guiwar UNICEF za su sa ido sosai tare da tabbatar da cewa babu wani yaro da zai bar garinsu har sai ya gama makarantar sakandare da firamare.

“Wadanda ba za su iya zuwa makarantar sakandare ba, za su sami damar zuwa makarantar koyon sana’a, ita ma kyauta ce.

“Saboda haka babu wasu iyaye da za su kawo mana uzurin cewa ‘ya’yansu baza su je makaranta ba,” cewar El-Rufai.

Ya godewa MHSSD da sauran hukumomin jihar akan jajircewar da suka nuna don ganin sun kyautata rayuwar yaran.

Ya kuma gode wa gidauniyar AMA da sauran kungiyoyi masu zaman kansu akan tallafin da suke baiwa gwamnati don baiwa almajiran kulawa da lafiya, abinci da sutura, da sauransu.

Haka kuma gwamnan ya jinjina wa UNICEF game da goyon bayan gwamnatin jihar wajen tabbatar da cewa an dauki komai bayanin kowanne yaro da aka dawo dashi daga wajen almajirancin.

El-Rufai ya ce kulawa da tallafin da aka bayar ya maido da martabar yaran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here