Babu marabar dambe da fada tsakanin Buhari da Hushpuppi, domin duka ‘yan damfara ne – Aisha Yesufu

0
405

Jigo a cikin kungiyar nan ta BringBackOurGirls, Aisha Yesufu, ta sake caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta ce shugaban kasar mai shekaru 77 tafiyar shi daya da fitaccen dan damfarar nan da aka kama a Dubai, wato Raymond Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

A cewar Aisha, babu gaskiya a cikin gwamnatin Buhari, kamar yadda aka sanya mutane suka yadda cewa komai ana yin shi bisa ka’ida ne, ta ce tun lokacin da ya ci zabe a shekarar 2015, Buhari bai bayyanawa duniya kudin da ya samu ba daga wajen al’umma wanda ya bukaci a taimaka masa zai yi yakin neman zabe da su.

Kwanan nan aka kama Hushpuppi a Dubai dake cikin babbar Daular Larabawa, a ranar 10 ga watan Yuni, kan zargin damfara, inda aka ce ya damfari mutane 1,926,400.

A wani rubutu da tayi a shafinta na Twitter, Aisha ta ce: “Da Buhari da Hushpuppi duka tafiyar su daya.

“Duka sun damfari miliyoyin mutane kudi! Ina kudin kamfen da aka tattarawa Buhari na 2015?

“Yayin da Hushpuppi shi damfarar kudi yayi kawai, shi Buhari biyu ya hada damfarar kudi da ta siyasa.”

Tuni dai gwamnatin tarayya tayi magana aka kama Hushpuppi da aka yi a Dubai.

Shugabar ‘yan Najeriya dake zama a kasashen ketare Abike Dabiri-Erewa, ta ce kada ayi amfani da abinda Hushpuppi yayi wajen yiwa ‘yan Najeriya dake zaune a kasashen ketare kudin goro.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here