Babu karya a maganar ciyar da dalibai a gidan iyayensu da muka yi – Sadiya Umar Farouq

0
504

Maganar ciyar da dalibai a gidan iyayensu da muka yi ba karya ba ce, cewar ministar cigaba da walwalar jama’a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Ta kare gwamnatin tarayya a ranar Alhamis, inda ta ce gwamnati za ta kashe naira miliyan dari shida da saba’in da tara a wannan shiri.

Ministar ta bayyana haka a jihar Legas a lokacin shirin raba kayan abinci ga dalibai na kasa da gwamnati ta gabatar a makarantar firamare ta St. Francis dake Maryland.

Ministar wacce ta samu wakilcin darakta ta ‘yan gudun hijira ta kasa Mrs Margaret Ukaegbu.

A cewarta ciyar da yara kanana a gidajen iyayensu shiri ne da ko ina a kasashen duniya aka yarda da shi domin tabbatar da yaran da iyayensu basu da karfi sun samu wadataccen abinci.

Ministar ta kara da cewa kasashe 16 da suka hada da Liberia da kasar Afrika ta Kudu, duka suna daga cikin kasashen da suke ciyar da dalibai a gidan iyayensu duk da an rufe makarantu.

‘Maganar ciyar da dalibai a gidan iyayensu ba magana bace sabuwa ko kuma ta kanzon kurege. Shiri ne da ya karbo a ko ina a kasashen duniya don tabbatar da yara sun samu isashen abinci a gidajen iyayensu,” ta ce.

Mataimakiyar shugaban kasa ta musamman, Mrs Titilola Adeyemi-Doro, ta ce a cikin gidaje 112,767 an ware gidaje 37,589, inda zasu more da romon wannan shiri a jihar Legas.

“Kamar yadda kowa ya sani dan abinda muke dashi a kasa ba zai yiwu ace mun ciyar da kowanne dalibi ba a makarantar firamare ta gwamnati, saboda haka shirin yana bin wata hanya ware wadanda suka fi kowa talauci don tallafa musu, wadanda suka hada da zawarawa, nakasassu, gidajen da masu gidajen suka rasa ayyukansu kuma basu da kudi da hanyar samun kudi, da dai sauransu,” ta ce.

Kowanne gida zai samu kilogiram 5 na shinkafa, kilogiram 5 na wake, karamar jarkar man gyada da karamar jarkar manja, gwangwanin timatir, kwai rabin kiret da kuma gishiri.

Shugaban ma’aikatar ilimi ta SUBEB ta jihar Legas, Wahab Alawiye-King ya ce shirin zai cigaba da wakana kowanne wata matukar ba a bude makarantu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here