Babu babban barawo irin ka – PDP ta mayarwa da Ganduje martani

0
439

Jam’iyyar PDP ta caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda a jiya ya ce jam’iyyar ta na goyon bayan Godwin Obaseki ne a zaben gwamnan jihar Edo da za ayi a watan Satumba saboda kawai suna hangen kudaden dake cikin baitul malin jihar.

A cewar Ganduje:

“Jam’iyyar PDP tana goyon bayan tsohon gwamnan jihar Edo ne bawai saboda suna da ra’ayi guda daya ba, sai dan kawai shine yake kula da kudin baitul malin jihar.”

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar a jiya da yamma, jam’iyyar PDP ta bayyana Ganduje a matsayin barawon baitul mali, wanda bai kamata ace har ya samu bakin yin magana akan cin hanci ba.

Jam’iyyar ta ce rainin hankali ne, ace mutum kamar Ganduje, wanda ya riga ya gama kunyata kanshi a idon duniya kan bidiyon ‘Gandollar’, bayan an kama shi yana karbar cin hanci, har ya samu bakin yin magana akan wasu suna so su kwamushe kudin baitul malin jihar.

PDP ta ce a gwamnatin Buhari ne kawai za a samu mutum irin Ganduje ya fito yayi magana a bainar jama’a, har ma ya jagoranci kamfen din kujerar gwamna.

PDP ta ce a bayyane yake, Ganduje da sauran shugabannin APC sun riga sun saba da satar dukiyar jama’a, wanda hakan shine babban abinda ke cikin ransa bayan an zabe shi a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zaben jihar ta Edo.

Ganduje ya kara tabbatar da ainahin manufar jam’iyyar APC, wanda shine amfani da dan takararsu wanda suke da hali iri daya, Osagie Ize-Iyanmu, don kwashe dukiyar jihar Edo, bayan gwamna Godwin Obaseki ya ceto jihar daga halin kaka-na-kayi da jam’iyyar APC ta saka ta a ciki.

Jam’iyyarmu tana tabbatarwa da Ganduje cewa babu wata dala da shi da shugabannin jam’iyyar APC za su samu a jihar Edo. Dukiyar jihar Edo da sauran jihohin PDP, dukiyar jama’ar jihohin ce ba ta kowanne dan siyasa ba. Kwarai kuwa hakane yasa mutanen jihar Edo suke nuna goyon bayansu ga Obaseki, saboda jayayya da yake yi da barayin APC. Haka kuma gwamna Ganduje da bidiyon shi na ‘Gandollar’ ba sa’an shugaban kwamitin yakin neman zaben PDP bane na jihar Edo, gwamna Nyesom Wike.

Saboda haka PDP ta shawarci gwamna Ganduje da APC da su cire tunanin sace dukiyar jihar Edo kamar yadda suke yi a sauran jihohin da APC ke mulki, saboda mutanen jihar Edo za su basu kunya a ranar 19 ga watan Satumba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here