Babu abinda Buhari ke yi sai kashe ‘yan Najeriya da haraji – Shugaban jam’iyyar PDP

0
328

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP, Prince Uche Secondus, ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da babbar jam’iyya mai mulki ta APC da sanyawa ‘yan Najeriya dan karen haraji tun lokacin da suka hau mulki.

Da yake magana ta wata sanarwa da mai taimaka masa a fannin sadarwa, Ike Abonyi ya fitar, ya zargi shugaba Buhari da kara sanya ‘yan Najeriya cikin tashin hankali da irin harajin da yake kara sanya musu, a lokacin da shugabannin wasu kasashen na duniya suke kokarin ganin sun taimakawa talakawansu.

A cewar shi, “wannan mataki da ya dauka yana sanya tattalin arzikin kasar cikin matsala, yana kashe kananan masana’antu, inda hakan ke sanya masu sanya hannun jari guduwa wasu kasashen don gabatar da kasuwancinsu.

“Abin yana bani dariya, yadda naga gwamnati tana ribanya haraji akan al’umma a wannan lokaci na annoba, maimakon kokarin ciro al’umma daga bakin talaucin da suke ciki, duka a karkashin gwamnatin Buhari.

Secondus ya lissafo wasu daga cikin abubuwan da suka kara kudin da suka hada da kudin man fetur, kudin wutar lantarki, kudin da ake cajar mutane a banki, da dai sauran su.

Sanarwar ta cigaba da cewa: “Wannan gwamnatin ta kara haraji daga kashi 5 zuwa kashi 7.5, bayan harajin N50 da babban bankin Najeriya ya saka a watan Janairun shekarar 2016; a watan Satumbar 2019, ta kara sanya haraji akan duka kudin da mutum zai cira banki da ya wuce N500,000, da kuma N3,000,000 ga kamfani.

“Bayan watan Fabrairun shekarar 2016, an samu karin kashi 45 cikin dari a kudin wutar lantarki, inda aka ce hakan zai sanya a samar da ingantaciyyar wutar lantarki. Gwamnatin ta sake sanar da sake duba dangane da wutar ta lantarki a ranar 1 ga watan Yulin wannan shekarar, yayin da wutar lantarkin ta kara lalacewa a kasar fiye da da.”

A cewar sa: “Da gangan gwamnatin shugaba Buhari take sanyawa ‘yan Najeriya wannan haraji don samar da kudaden shiga.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here