Babbar magana: Wata mata ta tona asirin kwamishinan ‘yan sanda da yayi mata ciki ya gudu ya bar ta bayan ta haihu

0
1014

Ms Wanger Eunice Iortile, mai shekaru 42 da Fatai Shittu, tsohon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Nasarawa, sun kwashe shekaru a baya suna yin soyayya wacce daga baya ta koma wani abu daban kuma. Ta dauki ciki tare da shi, bayan ta haihu sai ya gudu ya bar ta ya koma mahaifarsa can jihar Ogun a lokacin da yayi ritaya, inda ya bar ta ita da dan nasu wanda a yanzu haka yake da shekaru 8 a duniya.

A cewarta a lokacin da take soyayya da shi mata da yawa suna kishi a lokacin da suka je Abuja shekaru 17 da suka wuce. Sai dai ta ce shekaru 11 da suka wuce sune shekarun da baza ta taba mantawa ba a rayuwarta.

Ta ce inda ta sani, da tayi amfani da shawarar wani jami’in dan sanda da yayi ritaya da yace mata ta zubar da cikin.

Ta ce:

“Shittu shine mahaifin wannan dan nawa guda daya, amma ya gudu ya barni tun kafin ma na haife shi.

“Ni da dana mun sha wuya sosai, har ta kai ga akwai lokacin dana dinga tambayar kai na anya kuwa nice wacce nake matukar nunawa Fatai Shittu soyayya a baya?

Tana goge hawaye daga idonta a yayin da take bayanin, ta cigaba da cewa: “Shine babban abokina, kuma munyi soyayya sosai. Na fara haduwa da Fatai Shittu a Abuja (Wuse II) a shekarar 2003. Yana zama a gidan saukar baki na gwamnatin jihar Kwara, munyi soyayya ta tsawon shekara 9 kafin nan na samu ciki.

“Yana yiwa yayata da take sayar da kayan sanyi a Wuse II ciniki. A nan ne na hadu dashi muka fara soyayya.

“A lokacin da aka mayar da shi jihar Ebonyi a shekarar 2006, tare muka tafi can, inda muka shafe kusan shekara daya kafin nan aka sake dawo dashi Abuja.

“Na zama kamar matarshi a lokacin, saboda iyalan shi na jihar Ogun mahaifarsa.

“Mun shaku sosai, a wannan lokacin ban sake soyayya da wani namiji ba, har zuwa shekarar 2010 dana dauki cikin shi.

“Yayi ta yi mini barazana yayi kokarin sanyani na zubar da cikin naki yadda.

“Ya ce mini na zubar da cikin saboda ya kusa yin ritaya, kuma zai koma jihar Ogun ya cigaba da zama da iyalanshi.

“Da naki yarda na zubar da cikin, ya ce mini idan har na haifi mace zai karbe ta saboda bashi da ‘ya mace ko guda daya, amma kuma idan na haifi namiji ba zai karba.

“Bayan mun sha fama a karshe ya amince zai kula da dan koma wane iri ne. Kafin lokacin ya bani N30,000 na zubar da cikin naki yarda na zubar.

“A shekarar 2010 yayi ritaya daga aiki a matsayin kwamishinan ‘yan sanda a helkwatar ‘yan sanda ta Abuja.

“A lokacin da yake shirin komawa kauyenshi dake jihar Ogun, ya bani N150,000 domin na kula da kaina na fara kasuwanci, sannan yayi alkawarin kula da jaririn idan na haihu. A lokacin muna yawan waya tare.” Ta ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here