Babbar magana: Tuni na sadaukar da rayuwata ga Shaidan – Diane Kamsi

0
900

Wata budurwa mai suna Diane Emily Kamsi, ta bawa mutane mamaki bayan ta bayyana wanda ta sadaukar da rayuwarta a gare shi.

Diane ta bayyana cewa tuni ta sadaukar da rayuwarta ga shaidan, sannan ta kira wadanda suka zage ta a Facebook a lokacin da ta wallafa hakan.

A cewar dalibar dake a jami’ar Cape Town, ta ce ta riga da ta sayar da rayuwarta ga shaidan din saboda ba ta so ta shiga Aljanna ba tare da kudi ba.

A rubutun da ta wallafa, Diane ta bayyana cewa ranta na ta ne ita daya, saboda haka tana da ikon yin duk abinda take so tayi da shi, saboda haka shi yasa ta sadaukar da shi ga shugabanta.

Ta ce:

“Wawayen ‘yan Najeriya kawai marasa aikin yi, na sayar da rayuwata ga shaidan sai me? Rayuwata ce kuma rai na ne, saboda haka ina da ikon na sayar da shi ga duk wanda nake so. Ban son Aljanna ba tare da kudi ba.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here