Babbar magana: Tun ina ‘yar shekara 11 na shiga karuwanci – Kelly, wacce mahaifinta ya yiwa fyade tana shekara 5

0
2671

Wata budurwa da aka yiwa fyade tun tana ‘yar shekara 5 a duniya, ta gudu daga gidansu ta shiga duniya, don kada ta kara haduwa da mai yi mata fyaden, ta bayyana yadda ta fara karuwanci a lokacin da take da shekaru 11 a duniya.

Kelly mai shekaru 21 a duniya, ta bayyana yadda mutumin da ya reneta ya shigo dakin da take a buge a lokacin da take shekara 5. Lokacin tana kallon talabijin da matar da ta reneta, sai ya kira ta akan ta bishi zuwa dakinshi, inda ya fara yi mata fyade.

Budurwar ta bayyana cewa tun daga wannan lokacin ya dinga yi mata fyade, hatta matarsa da suke zaune tare ita ma ya dinga cin zarafinta, kuma babu abinda ta iya yi akan lamarin.

Kelly Photo Source: Facebook

A lokacin da take shekara 11 ta gudu daga gidan. A lokacin da take gudu ta hadu da wani mutumi da yayi mata alkawarin taimaka mata, amma a karshe sai ya koya mata karuwanci yake samun kudi da ita.

Daga baya ta samu ta gudu daga wajen shi, inda take zaune a wani waje, amma tana cikin damuwa akan tunanin kowanne lokaci mutumin da zai iya zuwa ya kashe ta.

Ta bayyana cewa bata yi makarantar sakandare ba. Tun da ta bar makarantar firamare lokacin da take da shekara 10 ba ta sake komawa ba. Ta ce tana bakin cikin yadda aka yi ba ta samu damar zuwa makaranta ba.

Budurwar ta ce babban burinta a rayuwa shine ta zama lauya, amma bata san yadda hakan za ta kasance ba a gareta.

Ta kara da cewa har yanzu tana jin kunyar kanta da kuma jikinta, kuma ta kara da cewa har yanzu tana cigaba da sayar da jikinta tunda shine kadai abinda ta kware a kai.

Ta ce an sha yi mata fyade, an yi mata duka hatta bindiga an saka mata a kanta anyi kokarin kasheta a lokacin da take yawo a titi.

Ta kara da cewa ta kuma yi tu’ammali da kwayoyi, har hodar iblis ta sha a lokacin da ubangidanta ya nuna mata, amma ta ce daga baya ta daina sha saboda tana neman haukatar da ita.

Kelly ta ce akwai lokacin da ta bugu ta fita ta fara yawo a titi tsirara haihuwar uwarta bata sani ba, sai daga baya ‘yan sanda suka kamata.

Budurwar ta bayyana cewa ta sha kokarin kashe kanta. Ta ce tana ganin bayan wannan hira da tayi da ‘yan jarida za ta iya kashe kanta, saboda bata da wani dalili na cigaba da rayuwa, bata da kowa bata da dangi, bata san abinda za tayi ba nan gaba, ta ce babu wani wanda ya taba nemanta.

Wannan hira da aka yi da ita an dauketa kwana daya kafin ranar kirsimetin shekarar 2019, amma an saki hirar a ranar 6 ga watan Yunin wannan shekarar ta 2020.

SKID ROW PROSTITUTE TELLS ALL

The streets are all she's known since she was 11. She didn't choose this life but it was her brutal reality for years.

Posted by In the NOW on Saturday, June 6, 2020

A lokacin hira da ita din budurwar ta bayyana cewa tana tunanin kashe kanta ne, saboda lokaci ne na kirsimeti amma ba ta da wani wanda za ta yi bikin wannan rana da shi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here