Babbar magana: Nan gaba tsirara zan fara fitowa a cikin wakoki na – Tiwa Savage

0
312
  • Fitaciyyar mawakiya Tiwa Savage, ta bayyana cewa a bidiyon da za tayi nan gaba za ta fito tsirara ne
  • Mawakiyar ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da BBC, inda ta ce a yanzu ba ta san wani irin salo za ta fito dashi da ya wuce wannan ba
  • Ta kuma nuna rashin jin dadinta akan irin halin kunci da talauci da al’umma suke ciki a wannan lokaci na Coronavirus

Fitacciyar mawakiyar kudancin Najeriya, Tiwa Savage, ta ce akwai yiwuwar nan gaba za ta fara fitowa tsirara a cikin wakokinta domin samun damar buge wakokinta na baya da tayi.

Mawakiyar mai shekaru 40 a duniya ta bayyana hakane a lokacin da take hira da BBC akan abinda mutane zasu iya gani nan gaba game da ita a sabon album da za ta fitar mai suna ‘Celia’

Ta ce, “ina jin zanyi bidiyo tsirara ne a nan gaba, saboda ban san wane irin abu zanyi ba da zai zama sabon abu ga mutane ba.”

“Kuma komai na cikin wakokin a Najeriya ne, daraktocin ‘yan Najeriya, komai daga Najeriya ne.

“Ina jin matukar dadi idan naga cewa komai na bidiyo din daga Afrika ne, kuma ‘yan Afrika ne suka yi, wannan shine abinda muka yi. Ina ganin idan kuka sanya kudinku a garemu zaku samu riba mai yawa.”

“A wannan lokaci da muke fama da annobar Coronavirus, abinda nake so nayi shine, ina so na sanar da su har yanzu nice shugaba, kuma har yanzu ina da kyau na, kuma har yanzu ni ‘yar Afrika ce.

“Mutane za su so shi sosai, Album din zai motsa zuciyar mutane da dama akan irin abubuwan da matan Afrika suke ciki: kauna, buri, da dai sauransu.

“Ina so nayi nuni da matan Afrika na zamani ne. Abin yana damuna matuka ganin yadda mutane ke shan wahala a wannan lokacin. Ina nufin mu Allah ya taimake mu, muna da wutar lantarki, muna da abinci da zamu ajiye na tsawon watanni idan muna so.

“Amma akwai mutanen da baza su iya ba, mutanen da iya abinda zasu ci a rana suke dashi. Wannan annobar ta bude mini zuciya na ga ainahin yadda duniyar nan take a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here