Babbar magana: Na gaji da shiriritar mijina shi yasa naje wani yayi mini ciki a titi – Matar aure ta sanar da alkali

0
298

Matar aure ta bukaci kotu ta raba aurensu da mijinta saboda ragontarsa a gado.

Matar mai suna Fumilayo Akinmulero ta bayyana yanayin zamanta da mijin nata mai suna Olusegun, inda take rokon kotu dake Badagry da ta raba aurensu na tsawon shekaru 11.

A cewar Funmilayo, mijin na ta ya taba kokarin kashe kanshi saboda rayuwa tayi masa wuya a wancan lokacin.

“Ya mai shari’a mijina yayi kokarin kashe kanshi har sau biyu, saboda rayuwa tayi masa wuya, ba tare da yayi tunanin ni da ‘ya’yanshi ba.

“A karon farko ya kawo maganin bera ya saka a abinci yaci, amma bai mutu, inda muka yi gaggawar kaishi asibiti.

“Bayan ya warke, kwanaki kadan ya kara cewa shi kashe kanshi zai yi sai ya dauki igiya ya shiga daji, makwabta suka je suka ceto shi.

“Ni ce nake daukar nauyin duka ‘ya’yanmu guda uku. Baya kula dani ko ‘ya’yanshi.

Funmilayo ta bayyanawa kotu cewa mijin nata ya taba kai mata hari a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2016, inda ya nemi kashe ta da adda, inda ta ce makwabta ne suka ceto ta.

“Mijina ya kawo wata gidanmu lokacin bana nan, bayan ya gama iskancinsa da ita, sai suka yi amfani da kayana suka goge jikinsu.

“Bayan na dawo naga abinda ya faru na tambayi abinda ya faru, sai ya mare ni ya dauko adda zai kashe ni.

“Bana son shi kwata-kwata yanzu, saboda akwai lokacin da ya karbi kudi a hannuna har dubu dari biyar ya gudu tsawon watanni shida bai dawo ba, ni kuma yanzu na samu wani har na samu ciki da shi.”

Funmilayo ta roki kotu akan ta raba aurensu ta kuma sanya Olusegun ya cigaba da daukar nauyin yaransu.

Olusegun wanda yake aikin kafintanci, bai samu damar halartar kotun ba domin kare kanshi.

A karshe dai alkalin kotun Mr. Shakirudeen Adekola, ya daga sauraron karar har zuwa ranar 18 ga watan Yuli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here