Babbar magana: Lokaci yayi da za a hana daukar ciki baki daya ga mata – Cewar Titania McGrath budurwa mai fafutukar kare hakkin mata

0
185

Wata budurwa mai fafutukar kare hakkin mata ‘yar kasar Amurka mai suna Titania, ta bayyana cewa lokaci yayi da za a hana daukar ciki baki daya ga mata, inda ta bayyana daukar ciki a matsayin hanyar azabtar da mata.

Titania ta wallafa wannan rubutu a shafinta na Twitter, inda ta ce karni da yawa da suka wuce an sanyawa mata sun yarda cewa dole ne sai sun haihu.

Titania ta ce:

“Karni da yawa da suka wuce ya mayar da haihuwa ba komai ba ga mata.

“Babu wani abu mai muhimmanci game da haihuwa, daukar ciki kawai wata hanya ce da maza ke bi suna azabtar da mata.

“Lokaci yayi da za a hana daukar ciki baki daya.”

To sai dai har ya zuwa yanzu babu wata kungiya ko hukuma da tayi magana dan gane da wannan rubutu na Titania McGrath, ma’ana babu wadanda suka nuna goyon bayansu ko akasin haka akan maganar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here