Babbar magana: Ko da aure ko ba aure sai na haihu nan da shekara 3 – Budurwa ta dauki hanyar yin cikin shege

0
304
  • A yanzu lokaci ne da mata da maza ba su damu da bayyana niyyarsu ko kuma bayyana cewa su mazinata bane
  • Domin kuwa wannan fitacciyar jarumar ta kudancin Najeriya ta bayyana cewa nan da wani lokaci koda aure ko babu sai ta haihu
  • Ta sanar da cewa a yanzu haka akwai wanda ya nemi aurenta, amma idan har bata aure shi ba nan da shekara uku sai ta haihu koma ta halin kaka ne

Tsohuwar jarumar wasan kwaikwayon Najeriya na Big Brother Naija, Iheme Faith Uloma, wacce aka fi sani da Ifu Ennada ta bayyana cewa nan da shekara uku za ta haihu ko da aure ko babu aure.

Budurwar ‘yar asalin jihar Abia, wacce ta fara tunanin yin aure kwanan nan, ta ce tafi son maza masu shekaru akan samari.

Ifu wacce ta bayyana cewa har yanzu babu wanda ya taba kwanciya da ita, ta ce: “Nan da shekara uku, zan haihu mace ko namiji koma tagwaye ne, kuma zanyi haka koda aure ko babu.”

“Ina da mutumin da ya nemi aurena. Muna soyayya shekaru da dama, kuma ya girme ni sosai. Nafi son tsofaffin mutane saboda sun fi samari sannin abinda suke yi. Samari wadanda suke da irin shekaruna sun fi gane rike wayar iPhone, daukar bidiyo a sanya a shafukan sadarwa da dai sauran su.” Cewar Ifu.

A daya bangaren kuma Press Lives ta kawo muku labarin fitacciyar mawakiyar nan ta kudancin Najeriya wato Tiwa Savage, wacce ta ce za ta dauki bidiyon wakarta tsirara nan gaba.

Mawakiyar ta bayyana hakane inda ta ce a yanzu ba ta san wane irin salo za ta zo dashi ba da zai taimaka mata ta kara samun mabiya fa masoya a wakokinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here