Tsugunne bata kare ba: Kasar Iran ta sanya a kamo mata shugaban kasar Amurka Donald Trump

0
1933

Kasar Iran tayi magana akan kisan babban janar dinta, inda ta bayar da sammacin kamo mata shugaban kasar Amurka Donald Trump.

Iran wacce kasa ce ta Musulmai tana neman taimakon kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa, wacce aka fi sani da suna INTERPOL, wajen kamo mata shugaban kasar na Amurka tare da wasu mutane da yawa.

Kasar ta Iran dai tana zargin su da kashe babban sojin ta a birnin Baghdad.

A cewar mai gabatar da kara na Tehran, Ali Alqasimehr, Trump, tare da wasu mutane sama da 30 suna da hannu a kisan da aka yi a ranar 3 ga watan Janairu, wanda yayi sanadiyyar kashe Janar Qassem Soleimani.

Saboda haka ana zarginsu da kisan kai tare da ta’addanci, a rahoton da kamfanin dillancin labarai na ISNA ya ruwaito.

Aljazeera ta ruwaito cewa Alqasimehr bai bayyana sunan kowa ba a cikin sauran mutanen banda na Trump.

Alqasimehr, ya ce Iran za ta cigaba da bin diddigin yanke masa hukunci har zuwa lokacin da zai gama mulki.

Har ila yau, ya kara da cewa Iran ta nemi a sanya sanarwa akan Trump da sauran mutanen. Wannan dai an ce shine mafi girman sanarwa da Interpol ta bayar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here