Babbar magana: Har sabuwar waya na siya saboda naje Kano naga Ado Gwanja – Budurwa ‘yar Kaduna ta shirya fito na fito da El-Rufai

0
230

A kokarin da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai yake na ganin ya dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar, gwamnan ya fito fili ya sanar da jama’a kudurinsa na hana sallar idi da kuma dokar hana fita da shigowa jihar har sai baba ta gani.

Wannan doka da gwamnan ya sanya dai bata yiwa mutane da yawa dadi ba, inda wasu da yawa suke ganin kamar an sanya dokar ne saboda a hana su zirga-zirga da kuma hana su bautar Allah.

Kamar yadda gwamnan ya bayyana a wani bidiyo da ya fito a wajen taron da ya jagoranta a jihar ya bayyana cewa:

“Zamu cigaba da sanya ido a jihar nan, saboda haka duk ma mai wani shirin zuwa daga Kano ya sani, ina nan ina jiran shi, kuma ba zan bar wurin ba sai dare yayi, saboda dole ne mu hana mutane wadanda su sunyi wasa da wannan ciwo yabi garinsu mu kuma su kawo mana shi.

“Dole ne mu kare al’ummar mu, abinda muke yi kenan, mutane da yawa baza su ji dadi ba, mutane da yawa suna zagin mu, akwai masu amfani da addini, akwai masu amfani da siyasa, wannan duk bai dame ni ba.”

Haka ita kuma a nata martanin wata budurwa ‘yar jihar da ta fito a wani sabon bidiyo, ta bayyana cewa Wallahi babu wanda ya isa ya hana ta zuwa jihar Kano, saboda haka za taje sai dai idan ta dawo ya hana ta shigowa Kaduna.

“Wallahi sai naje Kano, ina so zanje naga Ali Nuhu, na gama shiri zanje naga Ado Gwanja. Wallahi ko zai kashe ni sai naje Kano, sai dai idan na dawo ya hanani shigowa Kaduna.

“Ka ce akwai Covid-19 a Kaduna, ka hana mu fita yanzu sallah ta zo munce zamu je Kano ka hana. Na rantse da Allah har waya na canja ta daukar hoto idan Naje Kano.”

Ga dai bidiyon wanda tashar YouTube ta Tsakar Gida ta wallafa a shafinta:

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here