Babbar magana: Diyar tsohon shugaban kasa Obasanjo ta bariki ta bayyana a sabon bidiyo

0
839

Wani bidiyo na ta yawo na wata budurwa da tayi zargin cewa ita diyar tsohon shugaban kasar Najeriya cewa, Cif Olusegun Obasanjo.

Budurwar wacce ta bayyana sunanta da Faith, ta ce diyar tsohon shugaban kasar ce. A cewarta, kamar yadda akwai matan bariki na titi, haka akwai ‘ya’yan wadannan matan na bariki, ma’ana dai ita ‘yar shi ce ta bariki.

Budurwar wacce ta ce shekarar ta 21, ta ce tana zaune a kasar Spain ne, kuma ta yanke shawarar dawowa Najeriya shekarar da ta gabata. Ta cigaba da cewa, kuma ita ‘yar asalin Abeokuta da jihar Benue ce.

A cewarta, ita kayan da Obasanjo ya bari ce a jihar Benue. Faith ta ce ita da Obasanjo suna da matsala ta ‘ya da uba, inda ta ce kudin da tsohon shugaban kasar ya bata ya taimaka mata sosai, saboda yanzu haka ita ce shugabar Big Man Naija Reality TV, kuma ta mallaki otel da ta siya dala miliyan daya.

Ga dai biyon a kasa:

Mutane da yawa sun dauki wannan bidiyo abin dariya, saboda basu yadda cewa wannan budurwa ‘yar gidan Obasanjo ba ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here