Babban Farfesa dan kasar Japan ya Musulunta bayan yaci karo da wata Aya guda 1 ta Qur’ani

2
2601

Akwai mutane da yawa a duniya da suke ta faman cewa su basa bukatar addini saboda suna da fasahar zamani da kimiyya. Wani abin takaicin ma shine wasu Musulman da yawa sun fada cikin wannan tarko na shaidan, inda suke ganin Musulunci bashi da wayewa ta zamani.

Sai dai kuma duk da haka akwai masana da yawa da suka danganta abubuwa na kimiyya da fasaha da addini, inda wasu ma ke ganin dole sai sun danganta bincikensu da addini tukunna suke samun mafita.

Wani babban masanin kimiyya da fasaha dan kasar Japan ya karbi kalmar shahada bayan karanta Ayar Al-Qur’ani guda daya kawai.

Dr Atsushi Kamal Okuda, yayi rayuwa ta jahilci a baya, amma a yanzu ya musulunta. Kafin shigar shi Musulunci, Dr Okuda yayi rayuwa ta alfasha, ga rashin ilimin dalilin da ya sanya ya zo duniya.

‘Kafin na shigo Musulunci rayuwata bata da wata ma’ana, ga bakin jahilci, ban san gaskiya ba a lokacin!” inji Dr Okuda.

Ya fita neman addinin gaskiya har wani lokaci a lokacin da yake shekara ta shida a kwaleji, yaci karo da wata takarda a lokacin da yake bincike dake dauke da Ayar Al-Qur’ani, da take magana akan halittar dan adam da Allah yayi.

Inda Allah yake cewa: “Kuma lalle gaskiya ne mun halicci mutum daga yunbu.”

Wannan Ayah ta bashi mamaki sosai, sai tun daga nan ya fara bincike akan addinin Musulunci. Ai kuwa bai jima ba ya Musulunta, ya koma garin Aleppo na kasar Syria da zama domin ya koyi addinin Musulunci da kuma Larabci.

Yayi matukar farin ciki bayan komawarsa Musulunci, inda yayi bayani kamar haka: “A lokacin dana Musulunta, na san cewa wata baiwa ce Allah ya yiwa rayuwata.”

Yanzu haka Dr Okuda cikakken Musulmi ne, kuma babban Farfesa a bangaren ilimin siyasa a jami’ar Kieo dake Japan. Sannan kuma ya zama mai kiran mutane zuwa Musulunci abin koyi a wajen wasu kuma.

Dr Okuda ya dage kwarai da gaske wajen kiran mutane zuwa Musulunci, saboda ya san cewa duniyar ka iya shiga wani hali idan ba bi addinin Musulunci ba.

Komawar shi addinin Musulunci ya karawa mutane da yawa ‘yan kasar ta Japan da suke sha’awar shiga Musulunci fitowa fili suka bayyana imaninsu, inda kuma wadanda suke cikin addinin suka kara zage dantse.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here