Ba zan taba iya aurar mutum mai kudi kamar Dangote ba – Jaruma ta bayar da dalilanta

0
136
  • Jaruma Oyinkasola Emmanuel ta bayyana irin namijin da take so ta kari rayuwarta dashi
  • A cewar jarumar, tafi son mutum mai tsoron Allah wanda zai dinga ba ta lokacinta
  • Kai a karshe ma dai ta ce ita tana ganin ba za ta iya zaman aure da mutum mai kudi irin Dangote ba, saboda bashi da lokaci ko kadan

Fitacciyar jarumar fina-finan kudancin Najeriya, Oyinkasola Emmanuel, ta bayyana irin namijin da take so ta kari rayuwarta da shi, abin mamaki a ciki shine, mutumin da yafi kowa kudi a nahiyar Afrika baya cikin jerin mutanen da take sa ran zama da su.

A wani bidiyo da jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa ta san ita gajeriya ce, saboda haka tana son namiji dogo. Haka kuma ta bayyana cewa tana bukatar namiji mai tsoron Allah, wanda zai dinga ganin girmanta ya kuma kula da ita a koda yaushe.

Ta ce: “Zan so namiji mai tsoron Allah, wanda ya san darajar macen aure. Dole ya zama mai kamun kai, kuma yasan yadda ake tarairayar mace. Ban son mijin da zai koma kamar Mike Tyson ko Anthony Joshua a lokacin zaman auren mu. Haka kuma dole ya zama mai tsawo, saboda na san ni gajeriyace, idan na auri gajere irina zamu kare da haifar gajerun yara.”

Ta ce duk da tana son ta auri namiji wanda yake da rufin asiri, amma siffofin jikin namiji sun fi damunta fiye da kudinshi.

Ta kara da cewa baza ta iya auren mutum irin Dangote ba saboda bashi da lokaci a koda yaushe, inda ta ce babu wani kudi da zai saka mijinta ya dinga nesantar ta.

“Ba wai zancen dukiya bane ko kuma nasarar rayuwa, magana ce ta abinda mutum yake so. Ina so na samu irin namijin da nake so, babu wani abu da namiji zai nuna mini da zai sa naji na so shi indai baya cikin jerin mazajen da nake so. Kai hatta Dangote ba zan iya aura ba saboda bashi da lokaci, ba zai iya kula dani yadda ya kamata ba.

“Ba koda yaushe ne kudi yake biyan bukatar mutane ba, wani lokacin shi nake so a kusa dani. Ba wai nace bana son kudi ba, duk wanda zai aure ni dole ya zama yana da rufin asiri, dole ya zama yana da arzikin da zai iya lura da iyalinsa, ba wanda zai zame mini wahala ba. Koda bashi da miliyoyin kudin a yanzu zan iya tafiya da abina idan har yana cikin jerin wadanda nake so.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here