Ba zamu taba barin Igbo ya mulki Najeriya ba, saboda basu da amana – Shugaban matasan Arewa

0
1702

Shugaban matasan Arewa, Yarima Shettima, shine ya bayyana haka a lokacin da yake hira da manema labarai akan abubuwan dake damun Najeriya a wannan lokacin.

A cewarsa, “Muna fuskantar babbar barazana a Najeriya da ta sanya mutane da dama cikin hadari, sannan kuma da yawa sun rasa rayukansu, sanadiyyar wannan annoba ta coronavirus.

Yawancin kabilu na Najeriya sunyi iya bakin kokarinsu wajen taimaka game da yaki da cutar COVID-19, amma kowa ya sani cewa kabilar Igbo ne kawai aka barsu a baya, inda suka koma gefe suna ta faman kokari wajen ganin sun mulki Najeriya a zabe mai zuwa.

“Dukkan mu mun ga yadda Igbo suka koro almajirai, Fulani, kuma basa kaunar ganinsu a yankinsu har abada, amma duk da haka suna so su zo yankin mu su mulke mu. Mun riga mun gama yanke shawara babu wani kabilar Igbo da zai mulki Najeriya, saboda basu da amana, kuma koda mun basu dama, za su lalata komai a Najeriya ne.

“Duk wanda a cikinsu yake shirin fitowa takarar shugaban kasa, ya shirya fitowa domin ya fuskanci cin mutuncin da bai taba gani ba a rayuwarshi, mu ‘yan Arewa baza mu taba zabar dan kabilar Igbo ba a matsayin shugaban kasa,” ya ce.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here