Ba za mu taba samun kwanciyar hankali ba, saboda talaka na cikin wahala – Sanata Ndume

1
1125

Shugaban kwamitin hukumar tsaro na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya ce iya ‘yan majalisa da masu rike da madafun iko a kasar nan ne kawai suke samun albashi mai yawa a Najeriya.

Kamar yadda Punch ta ruwaito, Sanatan ya ce talakawa na cikin mawuyacin a wannan lokacin.

Ndume ya ce tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, abinda suka fada gaskiya ne akan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnatin kasar nan cikin tsadar rayuwa, inda suka ce idan har aka cigaba da haka babu abinda zai dore a kasar.

Sanata Ndume ya bayyana hakane a lokacin da yake mayar da martani ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Sanusi Lamido, yayin tattaunawa game da yadda za a daidaita tattalin arzikin Najeriya idan annobar coronavirus ta wuce.

Sanusi dai ya bayyana cewa yanayin yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya ba mai dorewa bane, inda yace lokaci zai zo da kasar za ta durkushe matukar ba a dauki mataki ba, inda ya tambayi mataimakin shugaban kasa akan abinda gwamnatin Najeriya take yi wajen shawo kan lamarin.

A yayin da yake mayar masa da martani, Osinbajo ya ce: ‘Ba sai an tambaya ba, kowa ya san cewa gwamnatin mu nada girma kuma komai na da tsada, amma kuma ‘yan majalisu ne za su iya rage tsadar gwamnati.

Ndume ya ce: “A cikin kasafin kudin Najeriya na tiriliyan 10 da aka fitar, kashi 30 zai tafi ga manyan ayyuka ne, kashi 70 kuma za ayi kananan ayyuka, yace wannan tsarin ba daidai bane ko kadan.

Ya ce: “Albashin da ake biyan ma’aikata iya na sayen abinci ne dana kashewa kawai, kadan ne daga cikinsu suke yin rayuwa mai walwala, dukkan mu ‘yan majalisar dattawa, mu ne ake bawa albashin da muke jin dadi a kasar nan.

“Daga yaya zamu ji dadi bayan kalilan daga cikin mu ne suke jin dadi, albashin dubu 30 mafi karanci yayi kadan, dole ne ma’aikata su koma karbar cin hanci da rashawa domin su tsira da rayukansu.

Ndume ya ce dole ne a canja yanayin yadda ake tafiyar da mulki a majalisar dattawan Najeriya saboda su kadai abin yake yiwa dadi a yanzu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here