Ba ni da damuwa, ko mai mata hudu na samu zan aura, babban abinda nake so shine soyayya – Jaruma

0
184

Kyakkyawar jarumar kudancin Najeriya, Christabel Egbenya, ta bayyana burinta na neman mijin aure koma wanene.

Jarumar ‘yar asalin jihar Enugu ta bayyana cewa yanzu ba ta da wani saurayi kuma a shirye take ta rungumi duk wanda ta samu a yanzu.

Ga abinda ta ce: “Idan ana zancen soyayya, a yanzu bani da wani kwakkwara a kasa, amma hakan ba yana nufin bani da saurayi ba. Ina son mutum mai kamun kai da fahimta. Ina son mutum da zai so ni a yadda nake kuma ya goya mini baya wajen kasuwanci na.

“Zai fi idan yana da dan arziki, sannan kuma kyakkyawa baki. Wane baya son abu mai kyau? Wannan ita ce addu’ar kowacce mace. Haka kuma zan iya aurar kowane yare. Ban damu ba ko Igbo ne ko Hausa, ko kuma Yoruba; idan har zan zauna lafiya da shi cikin farin ciki bani da damuwa. Zan iya zama da mai mata biyu, mai mata uku ko hudu, bani da damuwa idan har yana sona,” ta bayyanawa The Sun.

Dangane da yadda cutar Coronavirus ta taba harkar kasuwancin ta Christabel ta ce: “An kulle shagona, babu wata kasuwa babu kudi. Zaman da nake a gida shi yafi damu na, saboda babu wata hanyar da zanyi wani abu. Ina cikin matukar damuwa saboda babu kudi a wannan lokacin. Kayan dake cikin shagona sun fara canja kala, ina asarar miliyoyin kudi. Yanzu abinda nake yi kawai shine bacci, na tashi kuma na danyi atisaye na kuma yi addu’a.” ta ce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here