Ba kowanne alkalami ne zai iya rubuta irin shaukin da ake ji idan an shiga dakin Ka’aba ba – Evelyn Cobbold, Mace ta farko da ta fara Musulunta a kasar Birtaniya

0
385

Lady Evelyn Cobbold, ‘yar asalin kasar Scotland, ita ce mace ta farko da ta fara Musulunta a kasar Birtaniya, inda kuma ta zama mace ta farko da ta fara zuwa aikin Hajji bayan Musuluntar ta a kasar ta Birtaniya.

Evelyn ta fito daga babban gidane, inda taje aikin Hajjinta na farko a shekarar 1933, bayan ta nemi dama ta musamman daga wajen ministan kasar Saudiyya a birnin Landan.

Da yake a lokacin wadanda ba Musulmai ba, ba kasafai aka fiya barinsu su shiga birnin Makkah ba, amma Evelyn wacce ta canja sunanta zuwa Zainab, ta samu wannan alfarma daga wajen ministan Saudiyyar.

Shekara daya bayan ta dawo, Cobbold ta rubuta littafi.

“Ina cikin Masallaci a Makkah, cikin lokaci kankani sai naji komai ya canja mini saboda abubuwan mamakin dake ciki, ban taba tunanin ganina a waje irin wannan ba.”

Cobbold ta kari rayuwar kuruciyarta a kasar Algeria da Egypt, inda wata mata Musulma ta raine ta.

Ba ta bayyanawa duniya cewa ta Musulunta ba, har sai da ta shafe shekaru da dama, a lokacin da babban Pope na cocin Katolika ta duniya ya bukaci ya san inda ta saka gaba.

“Ban damu da sanin abinda yasa na canja addina ba, saboda ban taba tunani akan addinin Musulunci ba tsawon shekaru da dama. Kawai naji tunanin addinin ya zo mini ne, naga kuma ya kamata nayi nazari a kai, kuma nayi imani da shi.”

Bayan wannan hira da tayi da Pope dinne sai Cobbold ta yanke shawarar zuwa aikin Hajji.

“Mun shiga daki mafi tsarki, dakin Allah cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Hakika sai mutum ya samu alkalami na musamman zai iya rubuta irin shaukin da ake ji idan an shiga wannan waje.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here