Ba karamin sa’a muka yi ba da Allah ya bamu shugaban kasa irin Buhari – Femi Adesina

0
255

Babban mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara ta musamman a fannin sadarwa, Femi Adesina, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya sun yi babbar sa’a da samun shugaban kasa irin Buhari a wannan lokacin.

Femi Adesina ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, yayin da yake watsi da kokarin tursasa shi ya butulcewa shugaban na shi. A cewarshi, shi dan a mutun shugaba Buhari ne.

“Wani rubutu daga masu son tada zaune tsaye yana ta yawo, wanda aka sanya ni a ciki. Na yi dariya ne kawai. Ni dan Buhari ne a koda yaushe, bazan taba ja da baya ba, na yadda da shugaban kasar, kuma na yadda cewa yana jagorantar kasar nan akan hanya madaidaiciya.

“Maganar gaskiya ma munyi babbar sa’a da muka samu shugaban kasa irinshi a wannan lokacin. Duk wani kokari na bata ni da za ayi ba za ayi nasara ba.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here