Ayana Moon: Kyakkyawar jarumar fim ‘yar kasar Koriya ta karbi addinin Musulunci

0
1224

Idan zamu jero matasan mutane masu tashe wajen yada addinin Musulunci, wannan budurwar da zamu kawo muku labarinta za ta shiga cikin jerin su. Tana daya daga cikin matasa da suka yi nasara a rayuwa, kuma daya daga cikin mata masu tasiri a addinin Musulunci a duniya.

Ba kowa bace face Ayana Jihya Moon, fitacciyar mai amfani da shafin Instagram a kasar Koriya, An haifeta a ranar 28 ga watan Disambar shekarar 1995 a birnin Seoul dake kasar Koriya ta Kudu.

Ayana fitacciyar jaruma ce, sannan kuma tauraruwa wace tayi suna, tana da sama da mabiya miliyan uku a shafin Instagram, inda yawancin masu binta suka fito daga kasar Koriya, Indonesia da Malaysia.

Ayana tayi suna sosai duk da karancin shekarun da take da su. A yanzu haka tana aiki a matsayin tauraruwa dake tallar kaya na Musulmai, sannan kuma tauraruwa ce a wani babban kamfanin kayan kwalliya na kasar Indonesia.

Ayana ta samu wannan nasara daga Allah ne bayan Musuluntar ta shekaru 8 da suka wuce a lokacin da take da shekaru 16 a duniya. Ita ce mutum ta farko a danginsu da ta fara karbar Musulunci, inda daga baya dan uwanta Aydin Moon ya biye mata baya.

Ayana ta bayyana yadda ta Musulunta a wani daga cikin bidiyonta. A cewar Ayana, ta fara sanin addinin Musulunci ne a lokacin da take da shekara 7 a duniya, a daidai lokacin da ake yakin kasar Iraq.

Ta ce a lokacin ta san kasar Amurka sosai, saboda dangantakar dake tsakanin kasarta da Amurka, amma kuma bata san da kasar Iraq ba. A lokacin da ta fara hawa yanar gizo sai ta fara duba kasar Iraq.

Ta duba kasar Iraq da abinda yake faruwa a kasar. A lokacin ne ta fara ganin kalmar Musulunci. Ta gano cewa mutanen kasar Iraq suna bin addini mai suna Musulunci.

Ayana ta ce taji kalmar ta Islam tayi mata dadi sosai a baki. A wannan bincike da take yi ne ta gano hoton wasu matan Musulmai da suke sanya Hijabi da Niqab suna rufe jikinsu da fuskokinsu.

Ayana Moon wacce kakanta babban dan siyasa ne, tana yawan yi masa maganar Musulunci, akan Hijabi, Niqab da sauran su.

Mutanen kasar Koriya basu da masaniya akan Musulunci, kuma suna yiwa addinin wani kallo na daban.

Ayana dai abin yayi mata barkwakwai ganin cewa mata na rufe fuskarsu da jikinsu, taji tana son ta san wane daliline yasa suke hakan.

Ba kamar sauran mutane ba, Ayana ta cigaba da bincike akan Musulunci, inda a hankali ta fara son addinin. Ta kalli bidiyo kala-kala game da addinin Musulunci.

A lokacin yanda take yiwa Musulunci kallo shine akan yadda iyayenta suka sanar da ita, amma bayan yin bincike ta gano cewa ba haka Musulunci yake ba.

A hankali mutanen da take tare da su suka fara gane inda ta nufa. Sannu a hankali ta fara kalubalantar mutane game da ilimin addini.

A wannan lokacin ne Allah ya nuna yana da wani babban lamari akan ta. A lokacin da take makarantar sakandare, ta samu damar sanin Musulunci sosai. Ta shiga wata kungiya ta Musulmai matasa.

Kungiya ce da matasa suke koya da kuma koyar da addinin Musulunci ga mutane. A wannan lokacin ne ta fara zuwa Masallaci, inda ta hadu da wata yarinya karama da ta burgeta sosai.

A shekarar 2012, Ayana ta Musulunta, a farko ta fara jin tsoro kuma kanta ya daure game da sanya Hijabi kowacce rana. Ta samu dimuwa akan yadda za ta dinga yin ibada kowacce rana.

Ayana Moon tana son ta zama fitacciyar mace Musulma a duniya, kuma tana so ta cike gibin dake tsakanin kasar Koriya da Musulunci. Tana da kamfani na tafiye-tafiye, sannan ta kammala karatun digiri a jami’ar addinin Musulunci ta kasar Malaysia.

Ayana har littafi ta rubuta mai suna ‘Ayana’s Journey to Islam’ wanda mutane dama suka dinga saya suna karantawa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here