Asirin mai unguwa ya tonu, bayan an gano ya dirkawa budurwa ciki a daidai lokacin da ake shirin daura musu aure a bainar jama’a

0
1246

Asirin wani mai unguna ya tonu a lokacin da aka gano cewa ya dirkawa wata budurwa cikin shege.

An gano cewa budurwar na da dauke da cikin na tsawon wata uku lokacin da ake shirin daura mata aure a bainar jama’a wadanda suka halarci wajen domin shafa Fatiha.

Rahotanni sun bayyana cewa sama da shekara daya kenan mai unguwar Lugga dake cikin karamar hukumar Tongo, a yankin yammacin jihar Adamawa dake Arewa maso gabashin Najeriya, yana neman wannan budurwa da aure.

Sai dai kuma asirin su ya tonu, bayan an gano cewa budurwar wacce ya rage saura kiris a daura musu aure na dauke da juna biyu har na wata uku.

Sai dai mai unguwar da ake zargin ya dirka mata wannan ciki ya amince cewa zai aureta da cikin, inda su kuma iyayen yarinyar suka kekasa kasa suka ce ba za sabu ba.

A yayin da iyayen yarinyar suka ga cewa mai unguwar na neman yasa a rufe maganar, basu yi kasa a guiwa ba suka garzaya zuwa wajen kungiyar sasanta ma’aurata dake jihar Adamawa, wato Adamawa Concern Citizen.

A karshe dai kungiyar tayi alkawarin gabatar da kara a gaban kotu don kwatowa wannan budurwa hakkinta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here