Asiri ya tonu: An kama masu hakar kabari da kayuwan mutane guda biyar da suka tono a makabarta

0
2380

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta kama wasu masu hakar kabari guda hudu da suke aiki a makabartar karamar hukumar Akure ta Kudu dake jihar da kayuwan mutane guda biyar da suka tono a makabarta.

Mutanen da aka bayyana sunayensu da Kunle Olomofe mai shekaru 45; Adewale Abiodun mai shekaru 40; Akinola Sunday mai shekaru 69 da kuma Oluwadare Idowu mai shekaru 67.

Duka an kama su a lokacin da suka yanke kan wani direban tifa da da aka binne a makabartar lokaci kadan. ‘Yan uwan direban tifar sun je makabartar domin gyara kabarinsa inda suka ga cewa an fito da gawarsa daga cikin kabarin.

“Bayan mun kama su suna aikata laifin mun bincike su inda muka gano cewa ashe bayan wannan kan ma sun boye wasu kayuwan mutanen. Cikin gaggawa muka kira jami’an ‘yan sanda na SARS suka zo suka wuce da su,” cewar ‘yan uwan direban tifar.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, ASP Tee-Leo Ikoro ya ce yanzu haka sun fara gabatar da bincike akan wannan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here