Ango ya fadi ya mutu, bayan ya gogawa ‘yan daurin aure 100 coronavirus

0
1222

Wajen daurin aure a kasar Indiya ya juye ya zama wajen makoki, inda ango ya mutu sakamakon cutar coronavirus, sannan ya gogawa ‘yan daurin aure sama da mutum 100.

Hakan ya biyo bayan kin daukar shawara da dangin angon suka yi na cewa su daga bikin auren.

A rahoton da Hindustan Times ta fitar, mutumin mai shekaru 30, ya fara da zazzabi mai zafin gaske ne kafin auren na shi da aka yi a ranar 15 ga watan Yuni, amma dangin shi suka tilasta shi ya sha maganin da zai rage ciwon ayi biki a gama, wanda sama da mutum 360 suka halarta a garin Paliganj.

Bayan 48 ciwon yayi tsanani, inda ya mutu akan hanyar zuwa asibiti, a cewar majiyar. An kone gawarsa da gaggawa ba tare da yi masa gwajin coronavirus ba.

Sakamakon mutuwar da yayi, sai aka yiwa duk ‘yan uwanshi gwajin cutar ta coronavirus a ranar 19 ga wata, inda aka samu mutane 15 da suka kamu da cutar.

Don dakile yaduwar cutar, cikin gaggawa aka fara bi daya bayan daya ana yiwa mutanen da suka halarci daurin auren gwaji, inda aka samu mutane 86 da suka kamu da cutar, cewar wani jami’i a ranar Talata.

Sai dai ita kuma amaryar ba ta kamu da cutar ba.

“Duk da dai bashi da lafiya a ranar 14 ga watan Yuni, kuma ya bukaci a daga daurin auren, amma dangin shi suka ki yadda, inda suka bayyana cewa za su yi asara sosai, idan aka dakatar da bikin,” dangin angon ya sanar da Hindustan Times.

Wani dan uwan angon da bai kamu da cutar ba yace babu wanda yayi zargin cewa angon yana da COVID-19.

“Kamar yadda muka sani kauye ba sa fama da wannan cutar, hankalin mu a kwance,” cewar dan uwan angon.

“A ranar daurin auren jikin shi yayi zafi sosai, hakan ya sanya ‘yan uwa kowa ya damu, muka dinga addu’ar Allah yasa ba COVID-19 ba ce,” cewar dan uwan angon.

Wani jami’i a garin mai suna Chiranjeev Pandey, ya ce: “Abinda za mu yi yanzu shine dakile yaduwar cutar. Mun riga mun kulle duka wuraren da muke tunanin akwai cutar, ciki har da kasuwar Paliganj.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here