Ango da ya ciyo bashin naira miliyan 3 don hidimar biki, ya kashe kanshi, wata biyu da yin aure bayan amarya tayi masa bore

0
335

Wani sabon ango mai suna John Okpanachi ya kashe kanshi watanni biyu da yin aure sanadiyyar rikici da ya hado su da amaryarsa wacce ya ciyo bashin naira miliyan uku aka sha hidimar bikinsu da kudin.

Jaridar Within Nigeria ta ruwaito cewa mutumin mai yana aiki a daya daga cikin bankunan jihar Kaduna ne, inda ya mutu yana da shekara 37 a duniya.

A bayanin da dan uwanshi Micheal Okpanachi yayi, ya ce sun samu wata takarda a kusa da gawarshi dake bayyana cewa ya kashe kanshi ne sanadiyyar matsalar da suka samu shi da matarshi.

Micheal ya kara da cewa marigayin ya aro naira miliyan uku daga banki domin hidimar aurenshi.

An bayyana cewa marigayin John yana zaune a yankin Sabo ne kusa da hanyar Refinery dake Kaduna, ya auri amaryar shi daga Ankpa jihar Kogi, inda shi kuma ya fito daga karamar hukumar Ofu dake jihar ta Kogi.

Dan uwan marigayin yace ya samu matsala a aurenshi kwanaki kadan bayan sun tare da amaryarsa, inda ya bayyana cewa dan uwanshin yasha kiranshi a waya yana gaya masa abinda amaryarsa take yi masa.

Ya ce aurensu yazo karshe ne lokacin da matar marigayin ta turo shi daga cikin mota akan babbar hanyar Kaduna, inda tace ai motar kyauta ce da mahaifinta ya bashi a lokacin bikinsu, inda tace bashi da ikon tuka motar ba tare da amincewarta ba.

Micheal yace dan uwan nashi yayi fushi matuka akan abinda matar take yi masa, inda ya daina fitowa kwata-kwata sai labarin kashe kanshi da aka samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here