An yiwa matar dan siyasa dake da tsohon ciki fyade sannan an kashe ta a cikin gidanta

0
754

Mrs Queen Igbinevbo, matar Comrade Promise Igbinevbo wacce ke dauke da tsohon, an shiga har cikin gidanta an yi mata fyade sannan aka yi mata kisan gilla.

Mrs Igbinevbo na zaune ita daya a cikin gidanta dake Benin a lokacin da mutanen suka shiga cikin gidan nata taga cikin sili.

Wani wanda yayi magana da Linda Ikeji ya ce mutanen sun je gidan neman mijinta ne, wanda yake shine shugaban yakin zabe na dan takarar gwamnan jihar. Sai dai kuma bayan sun duba basu same shi ba, sai suka yi mata fyade suka kashe ta.

Matar wacce take da rikon addini, makwabtanta sun gano gawarta bayan sun shiga damuwa sanadiyyar daukar lokaci da suka yi ba tare da sun ganta ba.

Mutumin ya ce: “A lokacin da muka dauki lokaci bamu ga Queen ba, sai na zo don na duba naga ko lafiya, saboda ita daya tale zaune, mun tarar da ita tsirara, jini da kumfa na fitowa daga bakinta. Ga maniyyi nan duka a jikinta.

“Cikin gaggawa muka kira mijinta wanda yake zaune a wani waje.”

Mutumin da yayi magana da Linda Ikeji ya ce mutanen unguwar sun ga wani mutumi wanda basu saba gani ba a yankin yana ta kai kawo kwanaki kadan kafin a kasheta.

Kisan da aka yiwa Queen Igbinevbo, ta jawo zanga-zanga sosai a Benin. A ranar 5 ga watan Yuni, masu zanga-zangar sun garzaya har zuwa ofishin ‘yan sanda dake jihar Edo.

Mutumin da yayi magana da Linda ikeji ya bayyana cewa ya zuwa yanzu dai an kama mutane uku da ake tunanin suna da hannu da kisan nata.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here