An wayi gari wani mutumi ya tono gawar wani bawan Allah ya ajiye a gefen titi tana watangaririya

0
209

An tsinci gawar wani mutumi mai suna Isiuwa mai shekaru 82 a duniya, a gefen titi kusa da akwatin da aka binne shi a ciki, inda aka tono aka rufe kabarin aka ajiye shi a gefen titi.

A rahoton da Punch ta fitar, mutanen kauyen Umuoreihi dake karamar hukumar Umuahia ta Arewa dake jihar Abia sun wayi gari ranar Asabar suka tarar da gawar mutumin a gefen titi bayan mako biyu da mutuwarsa.

Wata majiya ta bayyana cewa mutumin da ya tono gawar ya tono ne a cikin daren ranar Juma’a a lokacin da ‘yan uwan mamacin suke bacci.

Majiyar ta bayyana cewa kafin a binne gawar Isiuwa, gawarshi sai da ta shafe shekara daya a asibiti kafin a karshe aka samu aka binne ta mako biyu da suka wuce.

Majiyar ta ce rikicin inda za a binne Isiuwa ne ya jawo aka yi ta bata lokaci har aka cinye shekara daya.

Dan gidan marigayin, Ebere, ya sanar da jaridar Punch sun wayi garin ranar Asabar suka tarar an cire gawar mahaifinsu kuma an mayar da kabarin shi an rufe.

A yayin da yake bayyana abinda zai yi akan wannan lamari, Ebere ya ce zai jira babban yayanshi da yayi tafiya ya dawo sai su sake binne mahaifin nasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here