An tono tsohuwa mai shekaru 79 daga kabari, bayan danta ya binneta da rai na tsawon kwana uku

0
245

Tsohuwa mai shekaru 79 a duniya ta sha dakyar bayan dan data haifa ya binneta a cikin kabari na tsawon kwanaki uku da ranta.

‘Yan sanda a yankin arewa maso yammacin kasar China, dake jihar Shaanxi sun ceto matar wacce barin jikinta ya shanye, mai suna Wang Mou, a ranar Talata 5 ga watan Mayu, bayan sirikar matar ta kai rahoton batan matar.

Dan nata mai shekaru 58, mai suna Ma Mou, an cafke shi da laifin kokarin kisan kai, a cewar ‘yan sandan yanzu haka suna gabatar da bincike akan lamarin.

‘Yan sanda na garin Jingbian sun bayyana cewa ranar Talata da misalin karfe 9 na safe, matar Ma Mou ta kai rahoto ofishinsu akan cewa mijinta ya dauki mahaifiyarsa a cikin a kwati da misalin karfe 8 na daren ranar 2 ga watan Mayu, amma tun bayan fita da ita ba ta dawo ba.

Ya ce ya bayyana mata ya kai mahaifiyarsa ziyara wajen ‘yan uwanta, amma kuma taji hankalinta yaki kwanciya da abinda ya gaya mata.

Bayan gabatar da bincike akan Ma, ‘yan sandan sun bayyana cewa ya gaya musu cewa ya binne mahaifiyarsa a kabari a kudancin garin Jingbian.

Bayan tabbatar da wajen da ya bayyana musu, sun tone kabarin inda suka tarar da matar a ciki tana kuka cikin abin tausayi. Abin ya basu mamaki yadda aka yi ta rayu ba tare da ruwa ko abinci ba na tsawon kwanaki uku.

Wani bidiyo ya nuna lokacin da suke ciro matar daga cikin kabarin, an garzaya da ita asibiti bayan an ciro ta daga cikin kabarin.

Yanzu haka danta zai fuskanci hukuncin kokarin kisan kai da gangan da ganganci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here