An sanyawa Masallaci sunan Sarkin Kiristoci saboda bawa Musulmai kariya da Sarkin yayi

0
681

Masallacin Al-Nejashi Masallaci ne da yake da dumbin tarihi a doron kasa. Masallaci ne da yayi nuni da cewa kowanne dan adam zai iya yin abu mai kyau a duniya.

An gina Masallacin a karni na 7, inda aka sanyawa Masallacin sunan Sarkin Kiristoci na Aksum wato Al-Nejashi. Hakan ya biyo bayan bawa Musulmai kariya da yayi a wancan lokacin.

A wancan lokacin Musulmai sunyi hijira zuwa kasarsa ciki kuwa hadda makusanta ga Annabi Muhammadu (SAW), inda ya taimaka musu ya basu kariya a lokacin da suke butakar hakan.

Bayan barin garin Makka, suka isa kasarshi, ya taimaka musu da zuciya daya yaki yadda ya bayar da su ga Kafuran Makka a wancan lokacin.

Press Lives ta kawo muku rahoton matashin saurayi Anthony Michael wanda ya wallafa yadda ya Musulunta a cikin watan Azumi na Ramadana.

Bayan wallafa hotuna masu ban sha’awa da yayi a shafinsa na Twitter a lokacin da yake karbar kalmar Shahada, Anthony ya bayyana irin farin ciki da annushuwa da ya tsinci kanshi a ciki bayan ya Musulunta.

Michael ya ce “Musulunci addini ne na soyayya da kauna, da kuma zaman lafiya,” inda ya ce kwanakin da suka gabata yana cikin jin dadi sosai.

Ya ce sakonnin da ya karba daga wajen ‘yan uwa Musulmai maza da mata sun kara saka masa nutsuwa da son addinin.

Ga dai cikakken labarin Anthony Michael: Matashin saurayi da ya Musulunta a watan Ramadana ya bayyana irin shauki da farin ciki da ya tsinci kanshi a ciki

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here