An sake yiwa wata dalibar kisan gilla a cikin coci bayan an yi mata fyade

0
469

Makonni kadan bayan an yiwa dalibar UNIBEN, Uwaila Omozuwa, fyade an kuma kasheta a cikin coci a jihar Edo, an sake samun wata dalibar mai suna Grace Oshiagwu, inda ita ma aka yi mata fyade sannan aka kasheta a cikin coci a garin Ibadan dake jihar Oyo, a ranar Asabar 13 ga watan Yuni.

A wani rahoto da muka samu, Grace mai shekaru 21 a duniya da take karatun difloma a kwalejin Oke Ogun, an yi mata fyade, sannan aka yi mata kisan gilla a wata coci dake Ojoo yankin Ibadan cikin karamar hukumar Akinyele. An samu gawarta da an sassara da adda.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Gbenga Fadeyi ya fitar, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce har yanzu suna tattara bayanai akan wannan lamari:

“Wasu da ba’a san ko su waye ba sun sassara wata mai suna Grace Oshiagwu, mai shekaru 21 a cikin coci dake Idi-Ori, kusa da babbar hanyar Shasha, a yau 12 ga watan Yunin shekarar 2020 da misalin karfe 3 na yamma.

“Tuni an fara gabatar da bincike akan lamarin, kuma jami’an ‘yan sanda sun fara neman wanda ke da hannu akan wannan lamari, yayin da muke wannan kokari zamu so mu samu cikakken bayani daga wajen mutanen wannan yanki dama jama’a baki daya don gano ainahin abinda yake sawa ake kashe mutane babu gaira babu dalili.” cewar Fadeyi.

Wannan shine dai karo na uku da aka yiwa daliba fyade kuma aka kasheta a jihar ta Oyo.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here