An kuma: Mata ta kashe mijinta bayan ta kama shi yana waya da budurwar

0
145

Jami’an tsaron Civil Defense reshen jihar Nasarawa, sun kama wata mata mai shekaru 22, mai suna Veronica Boniface, da laifin kashe mijinta kan ta kama shi yana waya da budurwarshi.

Da suke bincikar mai laifin a helkwatarsu dake Lafia, babban birnin jihar, kwamandan rundunar, Habu Fari, ya ce sun kama matar a garin Obene dake karamar hukumar Keana, bayan sun samu rahoton matar.

Kwamandan ya ce bayan gabatar da bincike akan matar sun gano cewa lafiyar ta lau ba ta da wani tabin hankali.

Haka kuma ya kara da cewa, da zarar sun kammala bincike a kan matar za su mika gaban kotu domin a yanke mata hukunci daidai da laifinta.

“An garzaya da mijin zuwa asibiti, bayan matarshi ta caka masa wuka a lokacin da rikici ya hado su akan kiran waya da take tunanin budurwarshi ce ta kira shi.

“Mun gano tana da jariri mai shekara biyu da rabi wanda a yanzu haka yake a wajen dangin mijin, mai suna Mohammed,” cewar Habu Fari.

Da take magana da manema labarai, Veronica ta bayyana cewa tayi dana sanin abinda ta aikata, kuma tana rokon ayi mata sassauci.

An kuma gano cewa matar na dauke da cikin wata daya ga marigayin.

Ta bayyana cewa shaidan ne ya rude ta har ta aikata wannan aika-aika, inda tace so tayi kawai ta tsorata mijin nata ta karbi wayar, sai tsautsayi yasa ta kashe shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here