An koma aure a yanar gizo a kasar Saudiyya bayan gwamnati ta hana daurin aure a kasar baki daya

0
415

Ma’aikatar shari’a ta kasar Saudiyya na koyawa mutane 5,000 darasi akan aure a yanar gizo, a kokarin da kasar take wajen mayar da aure a yanar gizo baki daya a fadin kasar.

Za’a koyawa mutanen yadda za su bayar da takardun aure ga ma’auratan ta yanar gizo ba tare da sunje kotu ba.

Takardar auren da za a dinga bayarwa a yanar gizo za ta dauki komai da komai dangane da ma’auratan guda biyu.

A yanzu haka dai ma’aikatar ta fara gabatar da gwaji a birnin Riyadh, inda ta saka ma’aikata 300 za su gabatar da auren mutane 2,000 tare da basu lasisin aure.

A ranar 12 ga watan Maris ne gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatar da duk wani aure a kasar, a kokarin da take na dakile yaduwar cutar Coronavirus a fadin kasar.

A ranar 26 ga watan Afrilu ne dai gwamnatin kasar ta cire dokar hana zirga-zirga da kasar ta sanya a birnin Makkah da wasu birane daban-daban.

Yanzu an bar mutane su dinga fita daga karfe 9 na safe zuwa karfe 5 na yamma har zuwa ranar 13 ga watan Afrilu, wato ranar da za’ayi azumi ashirin kenan.

A ranar 6 ga watan Afrilu ne dai kasar ta sanya dokar hana zirga-zirga a biranen Riyadh, Tabuk, Dammam, Dhahran, Hofuf, Jeddah, Taif, Qatif da kuma Khobar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here