An kashe babban likita an kone gawarsa a jihar Zamfara

1
7848

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta fara bincike akan kisan wani likita mai suna Enoch Okpara.

Okpara wanda yake babban likita ne a fannin mata da yake aiki a asibitin gwamnatin tarayya dake Gusau, an samu gawarsa a cikin gidansa dake unguwar Mareri dake cikin garin Gusau babban birnin jihar a ranar Asabar 13 ga watan Yuni.

An samu gawar marigayin a cikin gidan a kone kurmus, bayan cocin da yake zuwa ibada sun bayar da sanarwar batan shi bayan sun ga cewa bai je cocin ba a ranar Asabar da safe.

An ruwaito cewa shugabannin cocin sun sanar da abokanan aikin likitan halin da ake ciki, inda su kuma suka kira shi a waya, ta shiga amma ba a daga ba. Abokanan aikin da suke zargin akwai matsala sun duba gidanshi, inda suka tarar da motarshi a ajiye a tsakar gidan.

‘Yan sandan da suka samu nasarar shiga gidanshi bayan an sanar da su halin da ake ciki, sun iske gawarshi an kone ta an jefar da ita a bayan gidan shi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Shehu Mohammed, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Usman Nagogo tuni ya bayar da umarnin fara bincike akan wadanda suka aikata wannan aika-aika.

A wani labari makamancin haka mun kawo muku yadda wasu wadanda ba a san ko su waye ba suka kashe wata dalibar jami’a a bayan sun yi mata fyade a cikin coci.

Labarin kisan na ta yazo makonni kadan bayan kashe wasu daliban jami’ar guda biyu, wanda ya jawo aka fara zanga-zanga sanadiyyar wannan cin zarafi da ake yiwa matan.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here