An kasa samun fahimtar juna tsakanin Nazir Sarkin Waka da Hadiza Gabon kan matsalar fyade

0
686

Kamar yadda muka kawo muku yadda ake ta muhawara tsakanin masoya kuma abokan sana’a Nazir Sarkin Waka da jaruma Hadiza Gabon kan matsalar fyade da ta addabi al’umma, masoyan sun kasa fahimtar juna, inda kowa ya kafe akan ra’ayinsa.

Naziru yana ganin cewa laifin mata ne da suke fidda tsiraicin su, inda ya basu shawara da su dinga rufe tsiraicin su, kuma su kula da yaran su, sannan su hada da addu’a tunda Allah ne ya fada.

Ita kuwa Hadiza tayi tsalle ta dire tace sam maganar nan ta Nazir bata dace ba, domin hakan kamar yana nuna cewa masu fyaden basu da laifi kenan, inda take ganin akwai yara kanana da basu da wani abin sha’awa a jikinsu amma basu tsora daga wannan cin zarafi ba.

Sai dai Naziru yayi bidiyo, inda yayi jawabi ya kuma jawo aya ya fassara duk dan a fahimci manufar sa, koda yake dia jayayyar tasa da Hadiza bata fito sarari sosai ba, domin tun sanda Hadizan tayi masa tsokaci a kasan rubutun sa cikin bacin rai daga baya ta goge sai ya zamana sai dai kowa ya wallafa hujjojinsa a shafinsa.

Bayan Nazir yayi bidiyon sa na karshe yayi dogon jawabi Hadiza ta sake wallafa wani rubutu da ta kwafo daga wata mai amfani da shafin Facebook da yake kara jadadda hujjojin ta ga abin da rubutun ya kunsa.

Post source: Hadiza Gabon Instagram Page

A karshe Nazir din ganin fa baza a fahimce shi ba yasa ya kara wallafa cewa:

View this post on Instagram

Allah datar damu 🙏🏿

A post shared by Sarkin Wakar Sarki Sunusi II (@sarkin_wakar_san_kano) on

Post source: Nazir M Ahmed Instagram Page

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here