An kama tattabara da ake zargin ‘yar leken asiri ce a kasar Indiya

0
2491

Mahukunta a kasar Indiya sun ce tsuntsuwar da aka yi mata jan fenti, aka daura mata takarda da aka yi rubutu na sirri a jiki, an kamata a iyakar da ta raba kasar Indiya da Pakistan, kamar yadda rahoto ya nuna.

Mazauna kauyen Manyari dake kusa da iyakar sune suka kama wannan tsuntsuwa suka bayar da ita ga jami’an tsaro bayan sun kama ta a kusa da iyakar, kamar yadda Sky News ta ruwaito.

Geeta Devi, wacce ke zaune a garin Kathua dake yankin Kashmir, ta bayyana cewa tattabarar ta bi ta saman gidanta ranar Lahadi da daddare. ‘Yan sanda dai sun bayyana wannan tsuntsuwa da cewa ‘yar leken asiri ce, inda suka dukufa wajen gano sirrin wannan rubutu da aka kamata dashi a takarda, rahoton The Outlet.

“Bamu san daga ina tsuntsuwar take ba. Mutanen kauye ne suka kama ta akan katanga,” cewar shugaban ‘yan sandan kauyen Kathua, Sufuritanda Shailendra Mishra, ya bayyanawa jaridar Indiya ta The Times.

Bidiyon tattabarar kenan wanda Republic Media Network ta wallafa a YouTube

“Ana zargin tsuntsuwar ta kware wajen leken asiri ga kasar Pakistan, tana da zobe dauke da sako na wasika a jiki,” cewar dan sandan.

“Duk da dai tsuntsaye basu da wani shinge, da yawansu suna yawo daga wannan iyakar zuwa wata iyakar, amma wannan abu da muka gani a jikin tsuntsuwar shine ya zama abin lura a garemu, saboda ba kasafai zaka tsuntsu dauke da abu irin wannan a jikinshi ba,” cewar shi.

Sai dai kuma a wani rahoton, wani dan kauyen Pakistan ya bukaci firaministan kasar ta Indiya akan ya dawo masa da tsuntsuwar shi da aka kama a kasar da zargin cewa ‘yar leken asiri ce.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Habibullah, wanda yake zaune kimanin kilomita hudu tsakaninsa da iyakar, ya ce ya sanya tsuntsuwar ta tashi ne saboda yayi murnar ranar sallah.

Wannan dai ba shine karo na farko da aka fara amfani da tsuntsaye wajen leken asiri ba a kasashen duniya.

A shekarar 2016, ‘yan sanda a kasar Indiya sun kama wata tattabara dauke da rubutu da ake yiwa firaministan kasar Narendra Modi gargadi akan ajiye sojoji akan iyakar kasar Pakistan.

Haka a shekarar 2013, an kama wata tsuntsuwar da ta mutu dauke da karamar na’urar daukar hoto, a shekarar 2010 haka kuma an sake kama wata tattabara da take leken asiri duka a kasar ta Indiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here