An kama saurayi da ya yiwa mata sama da 40 fyade a Kano

0
374

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani mutumi mai shekaru 32, mai suna Muhammad Alfa, da laifin yiwa mata 40 fyade a cikin shekara daya a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da samun nasarar kama mutumin a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Kano.

Haruna ya bayyana cewa sun samu nasarar kama mutumin a ranar 10 ga watan Yuni, da misalin karfe 2 na dare. A lokacin da ya shiga wani gida a Kwanan Dangora dake Kano, da niyyar aikata wannan mummunan aiki.

Ya ce mutumin wanda aka fi sani da suna ‘Mai Siket’ ya saba shiga gidan mutane yayi musu fyade na tsawon lokaci, inda ya ce wasu daga cikin wadanda ya yiwa fyaden har canja masa suna suka yi suke kiranshi da Shaidan.

“Mutumin ya shiga wani gida a Kwanar Dangora, ya shiga dakin kananan yara, a lokacin da yake ciki mahaifiyar yaran ta ganshi sai ta sanar da ‘yan unguwa.

“Da farko ya samu ya gudu, amma kuma ‘yan unguwar sun samu nasarar kama shi, suka mika shi ga ‘yan sanda,” ya ce.

Haruna yace a yayin gabatar da bincike akan mutumin, ya bayyana cewa ya yiwa sama da mata 40 fyade a cikin shekara daya, yace wasu daga cikin wadanda ya yiwa din sun hada da yara kanana da kuma wata mata mai shekaru 80.

Ya ce tuni rundunar ta su ta fara samun korafi akan fyaden da wannan mutumi yayi.

Kakakin rundunar ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mr Habu Ahmad, ya bayar da umarnin mika mai laifin zuwa ga ofishin CID domin cigaba da gabatar da bincike a kanshi.

A cewar shi za a mika mai laifin gaban kotu da zarar an kammala bincike a kanshi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here