A yammacin ranar Litinin ne 1 ga watan Yuni, aka kama wani mutumi da laifin kashe kakarsa kuma yake cin namanta danye, lamarin da ya tada hankalin ‘yan sanda.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Dwayne Wallick, mai shekaru 37 an kama shi da misalin karfe 2 na rana, inda ‘yan sandan suka kama shi a lokacin da yake cin naman kakakar tashi mai suna Ruby Wallick.

A ranar Litinin da rana, mahukunta sun karbi kiran waya na 911, inda aka kai karar wani mutumi da yake tsaye akan wata mata a gida mai lamba 1200 dake Richmond. A lokacin da suka shiga gidan sun iske Dwayne Wallick tsaye akan gawar kakarshi yana cin namanta danye, kamar yadda Mercury News ta ruwaito.

Bayan ‘yan sandan sun iske shi sun bukaci ya daina cin naman, amma shi ko a jikin shi, ya cigaba da abinda yake yi. Dakyar ‘yan sandan suka samu damar saka masa ankwa, inda suka wuce dashi ofishinsu.

An kai Wallick asibiti inda ake tunanin ya dan samu matsalar kwakwalwa ne, cewar jami’an ‘yan sanda. Masu bincike suna duba akan ko abinda yayi din yana da nasaba da miyagun kwayoyi.

An ruwaito cewa na rasa wasu wurare a jikin matar mai shekaru 90. A lokacin da jami’an tsaron suka isa kuwa tuni har ta mutu, amma kuma ba a san ainahin abinda ya kashe ta ba.

Yanzu haka dai ‘yan sanda za su mika lamarin ga kotu inda za a yankewa Dwayne Wallick hukuncin wanda yayi kisan kai.

Duka Dwayne da kakarsa Ruby suna zaune a gida daya ne, a cewar ‘yan sanda. Inda suka kara nanata cewa har yanzu basu da masaniya akan mutuwar ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here